Gwamnan APC Ya Ba da Mamaki, Ya sake naɗa kwamishinoni huɗu da ya kora daga daga aiki
- Gwamna Aiyedatiwa na jihar Ondo ya maida mutum hudu daga cikin kwamishinonin da ya kora daga aiki
- Hakan na kunshe ne a jerin sunayen sabbin kwamishinonin da gwamnan ya aike ga majalisar dokokin jihar
- Bayan haka kuma gwamnan ya naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman a wata sanarwa da sakatarensa ya fitar yau Jumu'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya sake nada hudu daga cikin kwamishinonin da ya kora daga mambobin majalisar zartaswar jihar mako biyu da suka gabata.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutane huɗu da gwamnan ya naɗa na daga cikin jerin sabbin kwamishinonin da ya aike zuwa majalisar dokoki.
Makonni bayan korar dukkan hadimin tsohon gwamna, Aiyedatiwa ya miƙa sunayen mutanen da ya naɗa ga majalisa domin tantance su da tabbatar da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanda ya naɗa a matsayin kwamishinoni sun haɗa da Omowumi Isaac, Olukayode A. Ajulo, Razaq Obe, Emmanuel Igbassan, Akinwumi Sowore da Oseni Oyeniyi.
Sai kuma waɗanda suka sake komawa bayan korarsu da suka haɗa da Obe, Igbasan, Sowore da kuma Falana.
Gwamnan ya ƙara wasu naɗe-naɗe
Baya ga kwamishinoni, Gwamna Aiyedatiwa ya naɗa masu ba da shawara ta musamman har mutum uku.
Sun haɗa da Olugbenga Omole, a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, da Olamide Falana, a matsayin mai ba da shawara kan harkokin jinsi.
Na ƙarshen shi ne Alabi Johnson, wanda gwamnan ya naɗa a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan makamashi, The Nation ta rahoto.
Dukkan sunayen mutanen na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Prince Ebenezer Adeniyan, ya fitar ranar Jumu'a a Akure.
Wannan naɗe-naɗe na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Aiyedatiwa ya nuna alamun zai mayar da wasu daga cikin mambobin majalisar zartaswar jihar (SEC) da aka kora.
Matawalle ya soki dattawan Katsina
A wani rahoton kuma Bello Matawalle ya caccaki dattawan jihar Katsina kan barazanar da suka yi na juya wa Tinubu baya a zaɓen 2027.
Kungiyar dattawan Katsina sun yi barazanar janye goyon bayan Arewa ga Tinubu idan bai sauya tunani kan maida rassan CBN zuwa Legas ba.
Asali: Legit.ng