Atiku Ya Bayyana Ƴan Takarar da Yake Goyon Baya a Zaben da Za a Yi Ranar Asabar a Jihohi 9

Atiku Ya Bayyana Ƴan Takarar da Yake Goyon Baya a Zaben da Za a Yi Ranar Asabar a Jihohi 9

  • Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana waɗanda yake goyon baya a zaben cike gurbin da za a yi ranar Asabar a jihohi 9
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya aike da sako na musamman ga mazaɓar sanatan Ebonyi ta kudu
  • INEC ta shirya gudanar da zabukan maye gurbi domin biyayya ga umarnin kotu da kuma cike gurbin waɗanda suka yi murabus

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga al’ummar mazabar Ebonyi ta Kudu da su zabi dan takarar sanata a inuwar jam’iyyar PDP, Silas Onu.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaben 2023, ya roƙi mutanen mazaɓar Ebonyi ta kudu su kaɗa wa Mista Onu ƙuri'unsu a zaɓen cike gurbin da za a yi jibi Asabar.

Kara karanta wannan

Mutane sun fusata yayin da ake zargin wani mutumi ya yi ɓatanci ga Annabi SAW a jihar Arewa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Ya Bayyana Yan Takarar da Yake Goyon Baya a Zaben Cike Gurbi Ranar Asabar Hoto: @Atiku
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba yayin da ake shirin gudanar da zaɓen ranar 3 ga watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya zaɓe a mazaɓar ne domin maye gurbin David Umahi, wanda ya yi murabus, ya zama minista.

Atiku ya nuna goyon bayansa ga ƴan takarar PDP

A sanarwan da ya wallafa a shafinsa, Atiku ya ce mutanen mazaɓar Ebonyi ta kudu, majalisar dattawa da Najeriya baki ɗaya za su amfana da gogewar Onu idan ya samu nasara.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ba wai jihar Ebonyi kaɗai ba, yana kira ga dukkan mazaɓu 35 a jihohi 9 da kotu ta umarci a sake zaɓe da su kaɗa wa PDP kuri'unsu.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban majalisa ya faɗi wanda yake hangen zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027

Ya ce:

"Ina fatan masu kaɗa kuri'a waɗannan jihohi Ebonyi, Yobe, Borno, Kaduna, Benue, Ondo, Taraba, Lagos da Kebbi zasu sa kuri'unsu su tabbatar da cewa sun dawo daga rakiyar APC mai mulki."
"Haka kuma ina fatan zaɓen ranar Asabar zai gudana cikin lumana kuma INEC zata yi amfani da wannan dama wajen wanke kanta daga bakin fentin da ta shafa wa kanta a zaɓen 2023."

Gwamnatin Bauchi ta musanta hannu a kes ɗin Dutsen Tanshi

A wani rahoton kuma Gwamnatin Bauchi ta musanta hannun Gwamna Bala Mohammed a cafke fitaccen malamin nan, Sheikh Idris Dutsen-Tanshi.

Malamin mai ikirarin bin tafarkin aƙidar Sunnah na fuskantar shari'a a gabm kotu wanda ya kai ga kulle shi a gidan Kurkuku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262