Tsohon Hadimin Buhari Ya Yaba Kan Wani Abu 1 da Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yaba Kan Wani Abu 1 da Tinubu Ya Yi Wa Peter Obi

  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya yabawa tawagar Shugaba Tinubu kan yaɗa labarai bisa yadda suka sanya Peter Obi a inda ya dace
  • Ahmad ya ce fadar shugaban ƙasa na mayar da martani kan sukar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP yayin da ta yi shuru kan kalaman Peter Obi kan al'amuran ƙasa
  • A kwanakin baya Atiku da Obi sun yi Allah wadai da halin rashin tsaro a ƙasar nan, amma fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ne kawai ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bashir Ahmad ya nuna farin cikinsa kan yadda fadar shugaban ƙasa ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu ta ƙi mayar da martani ga Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani kan murabus da Atiku ya ce ya yi, ya aike masa da sako mai zafi

Ahmad, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 30 ga watan Janairu, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta sanya tsohon gwamnan jihar Anambra a inda ya dace ta hanyar yin shiru kan kalamansa kan al’amuran ƙasa.

Bashir Ahmad ya yabi Tinubu
Bashir Ahmad ya yaba wa Shugaba Tinubu kan kin kula Peter Obi Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi
Asali: Facebook

Sai dai tsohon hadimin na Buhari ya lura cewa fadar shugaban ƙasa ta mayarwa Atiku Abubakar martani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya yi kalamai sau tari kan kan al’amuran da suka shafi ƙasar nan.

Atiku, Obi, da Tinubu sun koma musayar yawu

Ku tuna cewa a kwanakin baya Atiku da Obi sun yi tsokaci kan halin rashin tsaro a ƙasar nan.

Yayin da Atiku ya nemi shugaba Tinubu da ya yi murabus idan har ba zai iya zama a ƙasar nan da kuma magance ƙalubalen da ta ke fuskanta ba, Obi ya koka kan yadda ake yin garkuwa da mutane da kashe-kashe tare da ziyartar iyalan waɗanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

"Idan ba za ka iya ba ka sauka": Atiku ya caccaki Tinubu kan abu 1 tak

Sai dai fadar shugaban ƙasar ta mayar da martani ga kiran na Atiku, inda ta ce har yanzu tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai warke ba kan kayen da ya sha a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Wane martani Bashir Ahmad ya yi?

Da yake magana kan musayar yawun da ake tsakanin Tinubu, Atiku da Obi, mai taimakawa tsohon shugaban ƙasar ya yabawa shurun da fadar shugaban ƙasa yi kan Peter Obi domin nuna masa ruwa ba sa'an kwando ba ne.

Bashir Ahmad ya rubuta a shafinsa na X cewa:

"Ina jin daɗin yadda fadar shugaban ƙasa ta sanya Peter Obi a daidai wurin da ya dace, duk da kalaman da ya ke yi tun bayan rashin nasararsa, kuma ba a taɓa mayar masa da martani kai tsaye ba. A halin yanzu dai Atiku ya riƙa samun martani ba ƙaƙƙautawa daga fadar shugaban ƙasa. Akwai bambanci kan yadda aka ɗauki kowa."

Kara karanta wannan

Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da aka nemi tsige Shugaban Ƙasa Tinubu

Bashir Ya Magantu Kan Sulhu a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi magana kan yin sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwaso.

Bashir ya bayyana sulhu tsakanin manyan ƴan siyasar biyu na jihar Kano zai amfani al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng