Majalisar Dokokin Jihar APC Ta Tabbatar da Tsige Shugaban Majalisar, Ta Rantsar da Sabo

Majalisar Dokokin Jihar APC Ta Tabbatar da Tsige Shugaban Majalisar, Ta Rantsar da Sabo

  • Magana ta ƙare, matakin tsige kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo, na nan daram
  • Ƴan majalisa 22 da suka halarci zaman yau Talata sun kaɗa kuri'ar amincewa da tsige shi bayan gabatar da rahoton bincike
  • Bayan haka kuma majalisar ta rantsar da sabon shugaban majalisar bayan gudanar da zaɓe kamar yadda doka ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Majalisar dokokin jihar Ogun ta tabbatar da tsige tsohon kakakin majalisar, Olakunle Oluomo a zaman ranar Talata, 30 ga watan Janairu, 2024.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, majalisar ta tabbatar da matakin ne yayin da gaba ɗaya mambobi 22 da suka halarci zaman suka kada kuri’ar amincewa da tsige shi.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ya fashe da kuka ana cikin zaman majalisa, an fadi dalili

Majalisa ta tabbatar da tsige shugaban majalisar dokokin jihar Ogun.
Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tabbatar da tsige kakaki, ta rantsar da sabon shugaba Hoto: Kunle Oluomo
Asali: UGC

Mataimakin kakakin majalisar, Bolanle Ajayi, mai wakiltar mazaɓar Yewa ta kudu a inuwar APC da, Musefiu Lamidi (APC-Ado Odo Ota 11), ne suka jagoranci zaman ƴan majalisar yau Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin zaman, Mista Ajayi ya karanto rahoton kwamitin da majalisar ta kafa domin ya gudanar da bincike kan zargin da ake wa tsohon kakakin majalisar.

Ya bayyana cewa kwamitin ya nuna wa tsohon kakakin cewa ba wai an kafa shi bane da wata manufa ta daban face ya yi adalci kan zargin da aka rataya masa.

Wane abubuwa kwamitin ya gano?

Da take jawabi kan binciken da aka yi, Lamidi ta ce kwamitin ya same shi da laifin aikata dukkan zarge-zargen da ake yi masa, don haka ta bada shawarar a tsige shi.

Bayan haka ta miƙa lamarin ga zauren majalisa wanda nan take yan majalisa 22 da suka halarci zaman suka amince da tsige Oluomu da ƙuri'u mafi rinjaye.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu ƙofar runtumo bashi a jiharsa, majalisa ta dakatar da ɗan majalisa kan abu 1

"Da kuri'un 'yan majalisa mafi rinjaye 22, na tabbatar da matakin tsige Oluomo daga mukamin kakakin majalisar dokokin Ogun," in ji ta.

An rantsar da sabon shugaban majalisar Ogun

Daga nan kuma sai Adegoke Adeyanju (APC-Yewa ta arewa 1), ya tsaida Oludaisi Elemide (APC-Odeda) a matsayin sabon kakakin majalisa kuma Adeniran Ademola (APC-Sagamu 11) ya goya masa baya.

Elemide ya yi rantsuwar kama aiki kuma an rantsar da shi a hukumance don maye gurbin shugaban majalisar da aka tsige, Daily Trust ta ruwaito.

APC ta gargaɗi Yahaya Bello?

A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC ya aike da saƙo ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan alamun da suka nuna yana son karɓe shugabancin APC.

A ranar Litinin aka ga wasu fastocin Yahaya Bello a wasu sassan Abuja waɗanda suka nuna yana sha'awar kujerar Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262