Gwamnatin Jihar Kogi Ta Kirkiri Sabon Ofishin Tsohon Gwamna? An Fayyace Komai

Gwamnatin Jihar Kogi Ta Kirkiri Sabon Ofishin Tsohon Gwamna? An Fayyace Komai

  • Yayin da ake ta yada jita-jitar cewa an kirkiri sabon ofishin tsohon gwamna, gwamnatin Kogi ta yi martani
  • Gwamnatin ta karyata labarin kirkirar sabon ofishin inda ta ce kawai wasu ne suka yada don biyan bukatar kansu
  • A ranar Litinin 29 ga watan Janairu ne aka yi ta yada cewa sabon gwamnan ya kirkiri ofishin tsohon gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta yi martani kan jita-jitar cewa ta bude sabon ofishin tsohon gwamna.

Gwamnatin ta karyata labarin kirkirar sabon ofishin inda ta ce kawai wasu ne suka yada don biyan bukatar kansu, cewar The Nation.

Gwamnatin APC ta yi martani kan jita-jitar kirkiro ofishin tsohon gwamna
Gwamnatin Jihar Kogi ya musanta kirkiro ofishin tsohon gwamna. Hoto: Usman Ododo, Yahaya Bello.
Asali: Twitter

Yaushe Ododo ya karbi mulkin Kogi?

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan yarjejeniyarsu da Tinubu don komawa APC, ya yi godiya

Idan ba a mantaba a ranar Asabar ce 27 ga watan Janairu aka rantsar da sabon gwamnan jihar, Usman Ododo bayan lashe zabe a watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya Litinin 29 ga watan Janairu ne aka yi ta yada jita-jitar cewa sabon gwamnan ya kirkiri ofishin tsohon gwamnan a gidan gwamnati.

Musanta zargin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a yau Talata 30 ga watan Janairu, cewar TheCable.

Martanin gwamnan kan jita-jitar

Sanarwar ta ce:

"Mun samu labarin jita-jita na yawo cewa Gwamna Ahmed Ododo ya kirkiri ofishin tsohon gwamnan a gidan gwamnati.
"Wannan labarin kanzon kurege ne da wasu makiya suke yi bayan ganin irin ayyukan alkairi da tsohon gwamnan, Yahaya Bello ya kawo a jihar.
"Abin takaici an kirkiri karyar ce don dauke hankali mutane amma ba su yi nasara ba saboda 'yan Najeriya su na da hikima."

Kara karanta wannan

Kamar Kano, Gwamnatin Kebbi ta fara yi wa zawarawa auren gata

Sanarwar ta kuma godewa 'yan jaridu kan binciken kwa-kwaf tare da tabbatar wa cewa labarin karya ne.

An rantsar da Ododo a matsayin gwamnan Kogi

Kun ji cewa a ranar Asabar 27 ga watan Janairu aka rantsar da sabon gwamnan jihar Kogi.

Alhaji Ahmed Ododo ya karbi rantsuwar kama mulki ne bayan yin nasarar a zaben da aka gudanar.

An kai ruwa rana a lokacin zaben inda Ododo da ya yi takara a APC ya buge sauran jam'iyyun SDP da PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.