Ministan Tinubu Ya Fara Shirin Murabus Daga Muƙaminsa Don Yin Takara? Gaskiya Ta Bayyana

Ministan Tinubu Ya Fara Shirin Murabus Daga Muƙaminsa Don Yin Takara? Gaskiya Ta Bayyana

  • Ministan bunƙasa harkokin ma'adanai na ƙasa ya nesanta kansa daga wasu fastoci masu nuna zai nemi takarar gwamnan jihar Ekiti
  • Dele Alake ya ce ko kaɗan ba shi da alaƙa da fastocin kuma ba ma ya sha'awar shiga takarar gwamnan jihar a zaɓe na gaba
  • A cewarsa, yanzu ya maida hankali kan ayyukan da ke gabansa a matsayin minista kuma yana goyon bayan Gwamna Oyebanji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dele Alake, ministan ci gaban ma'adanai na Najeriya ya ce ba shi da sha'awar tsayawa takarar gwamnan jihar Ekiti a zabe mai zuwa.

Ministan ya nesanta kansa da fastocin yaƙin neman zabensa da ke yawo a kafafen sada zumunta, ya ce ko alama bai san da zamansu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fusata, ya sanya dokar kulle a garuruwa biyu bayan faɗa ya kaure

Ministan ma'adanai, Dele Alake.
Dele Alake, Ministan Tinubu ya ce ba gaskiya bane wai zai nemi kujerar gwamnan Ekiti. Hoto: Dele Alake
Asali: Twitter

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ministan, Segun Tomori, ya fitar ranar Litinin, kamar yadda The Cable ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Mista Alake ya maida hankalinsa kacokan kan ayyukan da suka rataya a kansa a matsayinsa na minista, inda ya ayyana rahoton zai tsaya takara a matsayin ƙarya.

Tomori ya kara da cewa Alake yana goyon bayan gwamnatin Biodun Oyebanji, gwamnan Ekiti na yanzu, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Ministan wanda dan asalin jihar Ekiti ne, ya rike mukamin kwamishinan yada labarai da dabaru a Legas daga 1999 zuwa 2007.

Gaskiyar abin da ministan ya tunkara

Sanarwan ta ce:

"An jawo hankalin mai girma ministan ma'adanai Dakta Oladele Alake, kan wani fosta da ke yawo a soshiyal midiya da WhatsApp, wadda ta nuna shi a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ekiti."

Kara karanta wannan

"Ina cikin damuwa" Gwamnan PDP ya faɗi halin da yake ciki saboda rikicin siyasar jiharsa

“Muna sanar da ɗaukacin al'umma cewa Dakta Alake bashi da sha’awar tsayawa takarar gwamna a jihar Ekiti, ko yanzu ko nan gaba. Fostar da ke yawo kuma ba da yawunsa bane."
"Mai girma minista ya maida hankali wajen farfaɗo da harkar ma'adanai, nauyin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ƴa ɗora masa wanda ba zai ba shi damar tsayawa la'akari da zaben Ekiti ba."

Tinubu ya aika saƙon ta'aziyya ga Abdulsalami

A wani rahoton na daban Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar Hajiya Asabe, ƙanwar tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar a Abuja, inda ya yi addu'ar Allah ya gafarta mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262