Ba Shi da Tausayi, Gwamnan PDP Ya Yi Kaca-Kaca da Atiku Kan Dalili 1, Ya Yabawa Peter Obi da Tinubu

Ba Shi da Tausayi, Gwamnan PDP Ya Yi Kaca-Kaca da Atiku Kan Dalili 1, Ya Yabawa Peter Obi da Tinubu

  • Gwaman jihar Oyo, Seyi Makinde ya soki halin rashin tausayi na dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar
  • Makinde ya ce abin takaici ne Atiku ko kiransa bai yi ba don jajanta masa abin da ya faru a jihar na tashin bam
  • Legit Hausa ta tattauna da ɗan a mutun dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar kan wannan lamari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo – Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan rashin tausayi.

Makinde ya ce abin mamaki Atiku ko kiransa bai yi ba don jajanta masa abin da ya faru a jihar na tashin bam.

Kara karanta wannan

Ni yaso na gaje shi: Jigon APC ya fadi yadda suka yi da marigayi tsohon gwamna kafin rasuwarshi

Gwamnan PDP ya caccaki Atiku kan abu 1 kacal da ya faru
Gwamna Makinde ya soki Atiku kan rashin masa jaje. Hoto: Seyi Makinde, Atiku Abubakar.
Asali: Facebook

Mene Makinde ke cewa kan Atiku?

Ya ce dukkan wadanda suka yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun yi masa jaje kan abin da ya faru, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan Atiku yayin da ya karbi bakwancin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi.

Seyi ya ce tabbas akwai rashin tausayi game da abin da ya aikata inda ya ce hakan ya na nuna mummunan halin dan takarar na PDP.

Godiyar gwamnan ga Tinubu da Peter Obi

A cewarsa:

“Bari in yi amfani da wannan dama in godewa tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi.
“Na yi godiya ne saboda jajen da ya zo yi mana na musamman wanda babu siyasa a ciki.
“Ina kara godiya saboda duk wadanda suka yi takarar zaben 2023 sun mini jaje, shugaban kasa ya kira ni amma dan jam’iyyata Atiku bai kiran ko turo sako ba.”

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan kakakin majalisar da aka tsige

Makinde ya ce ya fadi haka a fili ne saboda ya sani cewa akwai lokacin siyasa sannan akwai lokacin yin shugabanci da kuma na tausayi, cewar OyoInsight.

Legit Hausa ta ji ta bakin ɗan a mutun tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kuma Zonal Coordinator na NECAF, Kwamred Aliyu Dyer.

Aliyu ya yi raddi kan kalaman Gwamna Makinde inda ya ce Atiku ba shi da irin wannan halin hatta wadanda ba 'yan PDP ba ma ya na musu jaje.

Ya ce kuma duk yakarsa da Makinde ya yi bai hana shi jajanta masa ba a shafin X kowa ya sani.

A cewarsa:

"Ina son in sanar da mai girma Gwamna cewa dukkan gwamnonin PDP da aka kai su kara zuwa kotu a kan zabe, bayan samun nasara mai girma Atiku Abubakar ya taya su murna.
"Kuma da iftila'i ya faru a jihar Oyo mu shaidane kuma al'ummar jihar ma shaidane duk da yakarsa da ya yi a zaben da ya gabata bai hana ya fito ya jajanta masa ba a shafin X.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

"A zaben da ya gabata ya shiga rigar PDP ya yaki dan takarar mu ya yiwa APC aiki yanzu muna kallo kuma a yanzu ba za mu zuba ma ido ba a ci gaba da cin mutuncin shugabanninmu muna kallo ba."

Mutane da dama sun mutu a Ibadan

Kun ji cewa, An shiga tashin hankali bayan abin fashewa ya yi sanadin mutane da dama a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Ana zargin abin fashewar ya tashi ne daga kamfanin hakar ma’adinai da ke yankin inda ya jawo asarar dukiyoyin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.