Ni Yaso Na Gaje Shi: Jigon APC Ya Fadi Yadda Suka Yi da Marigayi Tsohon Gwamna Kafin Rasuwarshi
- Yayin da ake daf da gudanar da zaben jihar Ondo, tsohon kwamishina ya bayyana yadda suka yi da tsohon gwamna
- Wale Akinterinwa ya ce gwamnan kafin rasuwarsa ya yi masa alkawarin shi zai gaji kujerarshi bayan barin mulki
- Marigayin tsohon gwamnan Rotimi Akeredolu ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disamba a kasar Jamus
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo – Tsohon kwamishinan kudade a jihar Ondo, Wale Akinterinwa ya bayyana abin da marigayi tsohon gwamnan jihar ya fada masa.
Wale ya ce marigayi Rotimi Akeredolu ya zabe shi a matsayin wanda zai gaji kujerarshi bayan ya sauka a mulki,cewar The Nation.
Mene jigon APC ke cewa a Ondo?
Idan ba a mantaba, Akeredolu ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disamba a kasar Jamus bayan ya sha fama da jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akinterinwa wanda har yanzu bai nuna sha’awar tsayawa ba ya ce Rotimi ya fada masa yiwuwar zai gaji kujerarsa bayan barin mulki.
Tsohon kwamishinan ya bayyana haka ne yayin hira da 'yan jaridu inda Rotimi ya umarce shi ya shirya gadar kujerar.
Alkawarin da marigayin ya masa
Ya ce:
“Mun yi zama da tsohon gwamnan a ofishinsa inda ya ce mini ya na fatan ni zan gaji kujerarsa.
"Ba zan iya rike ranar da hakan ya faru ba amma hakan ya faru ne jim kadan bayan dawowa daga jinya a Jamus.
"Ya yi min addu'a sosai ina tsammanin wasu sun san da maganar, nan da ba da dadewa ba zan sanar da neman takara ta."
Ya kara da cewa mutanen jihar sun aminta da shi don ganin ya cire musu kitse a wuta, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Dan takarar gwamna ya yi murabus
A wani labarin, yayin da ake daf da gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, dan takarar jam'iyyar LP, Azehme Azene ya yi murabus.
Azene ya bayyana haka ne ana daf da gudanar da zaben gwamnan jihar a watan Satumba.
Ya ce bai ji dadin abin da wani jigon jam'iyyar ya masa ba wanda hakan ne ya saka yanke shawarar.
Asali: Legit.ng