Abu Ya Girma: Ƴan Bindiga da Suka Sace Shugaban PDP Na Jiha Sun Aiko da Saƙo Mai Ɗaga Hankali
- Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da shugaban PDP na jihar Legas da wasu jiga-jigai sun nemi N200m a matsayin kuɗin fansa
- Mista Philip Aivoji da wasu mambobin PDP na hanyar dawowa daga Ibadan ranar Alhamis lokacin da ƴan bindiga suka sace su
- Jam'iyyar PDP ta yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnati a dukkan matakai su yi duk mai yiwuwa wajen ceto shi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Miyagun da suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Philip Aivoji, sun aiko da saƙon buƙatar a biya kuɗin fansa.
Masu garkuwan sun buƙaci a tattaro musu Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa kafin sako babban ɗan siyasan, cewar rahoton The Nation.
Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da Aivoji da wasu jiga-jigan PDP ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa maharan sace su ne a daidai yankin Ogere da ke kan babban titin Legas zuwa Ibadan, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Lamarin ya faru ne yayin da shugaban jam'iyyar tare da wasu ƙusoshi da ke cikin tawagarsa ke hanyar dawowa daga taron shiyya na masu ruwa da tsaki da ya gudana a jihar Oyo.
Ƴan bindiga sun turo saƙo mai ɗaga hankali
Wani mamban PDP da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun turo da saƙon adadin kuɗin da suke nema a matsayin fansa.
Ya ce sun nemi a zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansar sako jagororin babbar jam'iyyar adawa.
Tuni dai jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnatocin dukkan matakai su tashi tsaye wajen ganin sun ceto shugabanta.
A cewarsa, sace mutun kamarsa ya kara nuna yadda lamarin tsaro ya taɓarɓare a Najeriya da kuma bukatar ɗaukar tsauraran mataki domin magance matsalar.
An kashe shugaban tawagar ƴan bindiga
A wani rahoton na daban Ƴan sanda sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga mai garkuwa da mutane da wasu hatsabibai guda biyu a birnin Abuja.
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a Abuja ranar Jumu'a, 26 ga watan Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng