Babban Labari: An Yi Garkuwa da Shugaban Jam'iyyar PDP Na Jiha 1, Sahihan Bayanai Sun Fito
- Wasu miyagu sun yi awon gaba da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas, Mista Philip Aivoji ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu, 2024 da yammaci
- Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an sace jigon siyasar ne a kan titin Legas zuwa Ibadan da misalin karfe 6:00 na yammacin jiya
- Mai magana da yawun PDP na jihar, Hakeem Amode, ya yi kira ga hukumomin tsaro da gwamnati a dukkan matakai su shiga lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Lagos - Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na jihar Legas, Mista Philip Aivoji.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mahara sun yi awon gaba da shi ne a hanyar Legas zuwa Ibadan da misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis, in ji wasu majiyoyi.
Sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Honorabul Hakeem Amode, ya tabbatar da faruwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ya buƙaci hukumomin tsaro su tashi tsaye
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da hukumomin gwamnati a kowane mataki da su kawo ɗauki cikin gaggawa domin kuɓutar da shugaban jam'iyyar na jihar.
Amode ya bayyana cewa shugaban PDP na kan hanyar dawowa ne daga taron masu ruwa da tsaki a jihar Oyo wanda gwamnoni Seyi Makinde da Ademola Adeleke suka kira.
A rahoton Vanguard, kakakin PDP ya ce:
"Abin takaici ne yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kasarmu, kuma abin damuwa ne matuƙa yadda gwamnati ta gaza magance wannan matsalar.
"Garkuwa da Aivoji ya ƙara nuna matukar bukatar daukar kwararan matakai daga gwamnati da masu ruwa da tsaki don kawar da wannan matsalar.
"Muna rokon gwamnatocin jihohin Oyo, Ogun, da Legas, tare da jami’an tsaro, da su matsa kaimi wajen ganin an kuɓutar da shi lafiya ya koma cikin iyalansa da masu fatan alheri."
Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina
A wani rahoton kuma Miyagun ƴan bindiga sun kai hari kauyuka biyu a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, sun yi ajalin bayin Allah.
Rahoto daga mazauna yankin ya nuna cewa maharan sun sace mutane sama da 20 a hare-haren biyu da suka kai lokaci ɗaya.
Asali: Legit.ng