Gwamnan PDP Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Wike da Tinubu Bayan Nasara a Kotun Koli

Gwamnan PDP Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Wike da Tinubu Bayan Nasara a Kotun Koli

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya nuna farin cikinsa kan nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli a shari'ar zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamnan ya gode wa Allah, Shugaba Tinubu da ministan babban tarayya Abuja, Nyesom Wike bisa nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli
  • Fubara ya yi nuni da cewa zai cigaba da mayar da hankali kan harkokin mulki domin al'ummar jihar su kwashi romon dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya nuna godiyarsa ga Allah, shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, bisa nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli.

Gwamnan ya bayyana ƙudurinsa na ci gaba da tsayawa kan manufar da aka zaɓe shi a matsayin gwamna, inda ya ce babu abin da zai ɗauke hankalinsa a mulkinsa, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan tsohon gwamnan da ake tuhuma da wawushe N4bn

Fubara ya aike da sako ga Wike da Tinubu
Gwamna Fubara ya nuna godiyarsa ga Allah kan nasararsa a Kotun Koli Hoto: @govwike, @OfficialABAT, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Fubara ya jaddada ƙudirinsa na gudanar da shugabanci a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da zaɓensa matsayin gwamnan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce nasarar da ya samu a Kotun Ƙoli ta ta kawo ƙarshen ƙararrakin da suka dabaibaye gwamnatinsa cikin watanni takwas da suka gabata, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Su wa Gwamna Fubara ya gode wa?

Fubara ya nuna godiya ga Allah bisa taimakon da ya ba shi da kuma Shugaba Tinubu bisa rawar da ya taka a rikicin siyasar da kuma ƙararrakin da ake yi kan zaɓensa.

Gwamnan, a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Boniface Onyedi, ya kuma miƙa godiyarsa ga Wike, wanda ya bayyana a matsayin “Oga”, bisa dukkan goyon bayan da ya bayar.

Kara karanta wannan

Ana cikin rade-radin dawowar Ƙwankwaso APC, Ganduje ya sha sabon alwashi kan abu 1

Gwamnan ya yi kira ga kowa da kowa da ya haɗa hannu da gwamnatinsa don gina jihar ta yadda za a samu ci gaba ta kowanne fanni.

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Zaɓen Gwamna Fubara

A baya rahoto ya zo cewa Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe kan sahihancin zaɓen Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Kotun ta tabbatar da nasarar gwamnan tare da yin watsi da ƙarar da jam'iyyar APC ɗan takararta suka shigar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng