Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Sabon Mataimakin da Gwamnan APC Ya Nada

Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Sabon Mataimakin da Gwamnan APC Ya Nada

  • Majalisar dokokin jihar Ondo ta kammala aikin da Gwamnan jihar Lucky Aiyedatiwa ya ba ta na tantance sabon mataimakin gwamnan jihar
  • Majalisar dokokin bayan kammala tantacewar ta amince da naɗin da gwamnan ya yi wa Olayide Adelami a matsayin mataimakinsa
  • Sabon mataimakin gwamnan ya sha alwashin yin aiki tuƙuru tare da ba mara ɗa kunya a sabon muƙamin da aka ba shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - A ranar Alhamis majalisar dokokin jihar Ondo ta tantance tare da tabbatar da Olayide Adelami a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo.

Wannan ci gaban ya zo ne sa'o'i 24 bayan gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa ya zaɓi Adelami a matsayin mataimakin gwamna, kuma ya aika sunansa ga majalisar domin tantancewa da amincewa da shi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya aike da muhimmin sako ga Wike da Tinubu bayan nasara a Kotun Koli

Majalisa ta amince da nadin Adelami
Majalisar dokokin jihar Ondo ta amince da nadin Adelami a matsayin mataimakin gwamna Hoto: Hon Lucky Aiyedatiwa, Olayide Owolabi Adelami
Asali: Facebook

Majalisar ta tabbatar da wanda aka naɗa ne bayan nazarin rahoton kwamitin zaɓen majalisar wanda shugaban majalisar, Mista Olamide Oladiji ya jagoranta, a yayin zaman majalisar, rahoton Channels tv ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko majalisar ta gudanar da aikin tantance wanda aka naɗa a harabar majalisar kafin zamanta.

A yayin zaman majalisar, magatakardar majalisar, Jaiyeola Benjamin ya karanta wasiƙar da gwamna Aiyedatiwa ya aike wa majalisar domin tantance wanda aka naɗa.

Majalisa ta amince Olayide ya zama mataimakin gwamna

Shugaban majalisar, Oladiji wanda ya yanke hukuncin tabbatar da wanda aka naɗan, ya taya mataimakin gwamnan murna, inda ya buƙace shi da “ya yi iya bakin ƙoƙarinsa".

Ya kuma yi alƙawarin goyon bayan majalisar ga ɓangaren zartarwa domin jama’ar jihar su ci moriyar dimokuraɗiyya.

A nasa martanin, Adelami ya yabawa Gwamna Aiyedatiwa kan naɗin da ya yi masa, inda ya yi alƙawarin ba zai ci amanar amincewar da aka yi masa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya shiga matsala bayan kotu ta tura yan a mutunsa gidan yari, ta fadi dalili

Gwamna Aiyedatiwa Ya Kori Kwamishinoninsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, ya rusa dukkan majalisar zartaswar jihar nan take.

Gwamnan ya kuma kori dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da hadimai na musamman manya da ƙanana a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng