Gwamnan APC Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamna a Jiharsa

Gwamnan APC Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamna a Jiharsa

  • A karshe, gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya bayyana wanda yake so ya zama mataimakinsa
  • Aiyedatiwa ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami, a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu
  • Sabon mataimakin gwamnan ya kasance magatakardar majalisar tarayya mai ritaya kuma ya yi takarar gwamnan jihar a 2020 amma ya janyewa marigayi Akeredolu
  • Hakan na zuwa ne kasa da awanni shida bayan gwamnan ya rushe mambobin zauren majalisar da magabacinsa, marigayi Rotimi Akerolu ya nada

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya bayyana wanda yake so ya zama mataimakinsa.

Aiyedatiwa ya nada tsohon mataimakin magatakardar majalisar dokokin tarayya, Cif Olayide Owolabi Adelami, a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ondo, jaridar Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnan APC ya kori kwamishinoni da masu mukamai da mai gidansa ya nada, akwai dalili

Gwamnan Ondo ya bayyana mataimakinsa
Gwamnan APC Ya Nada Sabon Mataimakin Gwamna a Jiharsa Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Nadin Adelami na zuwa ne kimanin awanni shida bayan gwamnan jihar ya tsige yan majalisar zartarwa na jihar a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewat sanarwa daga babban sakataren labaran gwamnan, Mista Ebenezer Adeniyan, an mika sunan sabon mataimakin gwamnan zuwa zauren majalisar dokokin jihar don amincewa da shi, rahoton Punch.

Sanarwar ta ce:

"Majalisar dokokin za ta sanar da nadin nasa a yau."

Wanene sabon mataimakin gwamnan Ondo?

Adelami ya yi ritaya a matsayin mataimakin magatakardar majalisar tarayya a watan Afrilun 2018. Ya fito daga yanki daya da marigayi tsohon gwamna Rotimi Akeredolu, karamar hukumar Owo.

Adelami ya yi takarar tikitin gwamnan APC a 2020 amma ya janyewa marigayi Akeredolu.

Aiyedatiwa ya kori yan majalisa da Akeredolu ya nada

A baya mun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya rusa dukkan majalisar zartarwa a jiharsa, kamar yadda NTA News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Za a yi jana'izar gwamnan APC da ya rasu a kan Mulki, sanarwa ta fito

Gwamnan ya kuma rusa dukkan mukaman siyasa da suka hada da hadimai na musamman manya da kanana a jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Ebenezer Adeniyan ya fitar a yau Laraba 24 ga watan Janairu.

Sanarwar ta bukaci dukkan wadanda aka sallama su mika takardun ofisoshinsu ga sakatarorin din-din-din a ma'aikatunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng