Tafiyar Tinubu Zuwa Faransa Ta Bar Baya da Kura Yayin da PDP da LP Suka Yi Masa Tonon Silili

Tafiyar Tinubu Zuwa Faransa Ta Bar Baya da Kura Yayin da PDP da LP Suka Yi Masa Tonon Silili

  • Jam'iyyun PDP da LP sun fito sun caccaki tafiyar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi zuwa Faransa
  • Jam!iyyar PDP ta yi nuni da cewa tafiyar ta zo a lokacin da bai dace ba domin ƙasar nan tana buƙatar shugabanta a halin yanzu
  • Ita kuwa jam'iyyar LP ta yi nuni da cewa shugaban ƙasar bai da lafiya ne shi ya sa ya fice ya bar ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam'iyyun PDP da LP a ranar Laraba, sun buƙaci a yi musu ƙarin bayani yayin da Shugaba Tinubu ya shilla zuwa ƙasar Faransa, domin yin wata ziyara ta ƙashin kansa.

Mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa tafiyar ta sa ta zo a lokaci mafi muni na fama da rashin tsaro da matsalar tattalin arzikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mata da miji da yaransu a Kaduna

An caccaki tafiyar Tinubu zuwa Faransa
PDP da LP sun kalubalanci tafiyar Tinubu zuwa Faransa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Shi ma kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaben shugaban ƙasa na LP a zaɓen 2023, Yunusa Tanko, ya yi zargin cewa akwai wata ɓoyayyar manufa kan tafiyar tare da ambaton cewa shugaban ba shi da lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Laraba ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa domin wata ziyara ta ƙashin kansa.

Wane irin martani PDP da LP suka yi?

Da yake mayar da martani, mataimakin sakataren na PDP, Abdullahi, a wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar The Punch, a ranar Laraba, ya ƙalubalanci fadar shugaban ƙasa da ta fito ta faɗi gaskiya kan tafiyar Tinubu zuwa Faransa.

A kalamansa:

"Abin da mu ke ji shi ne shi (Tinubu) ya tafi jinya kamar yadda ya saba domin a can ne likitocinsa suke. Don haka muna ƙalubalantar fadar shugaban ƙasa da ta fito ta kuma yi mana bayanin irin ciwon da yake fama da shi."

Kara karanta wannan

Ana cikin rade-radin dawowar Ƙwankwaso APC, Ganduje ya sha sabon alwashi kan abu 1

Kakakin na LP, Tanko, ya bayyana tafiyar Shugaba Tinubu a matsayin abin da ba za a amince da shi ba.

A cewarsa:

"Mun sake samun wani Muhammadu Buhari, wanda ya zaɓi ya riƙa tafiye-tafiye fiye da shugabanci. Maganar gaskiya ita ce Tinubu bai da lafiya kuma suna ƙoƙarin yin rufa-rufa ne.
"Lokaci na ƙarshe da muka ganshi shi ne lokacin da ya je Imo. Sannan na lura cewa hannuwansa suna rawa. Hakan ya isa ya nuna maka cewa akwai alamar tambaya kan lafiyarsa."

Tinubu Ya Nemi Goyon Bayan CAN

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi samun goyon baya daga wajen ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN)

Shugaban ƙasar ya nemi goyon bayan ne domin yaƙar cin hanci da rashawa da suka yi wa ƙasar nan katutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng