Ganduje Ya Isa Jihar Kano, Zai Gana Da Masu Ruwa da Tsaki Kan Batun Sasantawa da Kwankwaso
- Shugaban jam'iyyar APC mai mulki na kasa, Abdullahi Ganduje ya dira a jiharsa ta Kano a yammacin Laraba, 24 ga watan Janairu
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin sulhunta tsakanin Ganduje da tsohon ubangidansa, Sanata Rabiu Kwankwaso
- Ganduje zai kuma gana da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a ranar Alhamis, 24 ga watann Janairu kan batun sulhu da bangaren Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Kano, jihar Kano - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya isa jihar Kano a yammacin ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
Ganduje ya isa filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da misalin karfe 7:30 na yamma sannan ya samu tarba daga mambobin jam'iyyar APC.
Ganduje zai gana da masu ruwa da tsaki
Jaridar Legit Hausa ta fahimci cewa an shirya Ganduje zai gana da manyan masu ruwa da tsaki na APC a jihar Kano, a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu a sakatariyar jam;iyyar dake jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron wanda aka shirya yi da rana, yana nufin magance kokarin da ake yi na sasanta wasu masu ruwa da tsaki a siyasa ciki harda yan adawa da ke da ra’ayin komawa jam’iyyar APC.
Musamman dai manyan masu goyon bayan abokin hamayyar Ganduje, Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso, tsohon ubangidan Ganduje kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a zaben 2023, yana jagorantar tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano.
Jam'iyyar APC reshen Birtaniya, ta yada bidiyon Ganduje a lokacin da ya isa jihar Kano a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) haka kuma jigon jam'iyyar, Imran Muhammad ma ya wallafa shi.
Kalli bidiyon Ganduje a lokacin da ya isa filin jirgin sama a kasa:
An yi arangama tsakanin yan NNPP da APC
A wani labarin, mun ji a baya cewa magoya bayan manyan jam'iyyun siyasa masu hamayya da juna a Kano na ci gaba da arangama da juna a wasu sassan jihar a ƴan kwanakin nan.
Legit Hausa ta tattaro cewa jam'iyyun NNPP mai mulki da APC na ci gaba da zaman doya da manja a jihar, duk da har yanzun ba a rasa rai sakamakon rikicin ba.
Asali: Legit.ng