Ma'aikatan Gwamnati Sama da 200 Sun Shiga Tasku Yayin da Aka Dakatar da Biyansu Albashi Kan Abu 1

Ma'aikatan Gwamnati Sama da 200 Sun Shiga Tasku Yayin da Aka Dakatar da Biyansu Albashi Kan Abu 1

  • Gwamnatin Yahaya Bello na jihar Kogi ta dakatar da biyan albashin ma'aikata 231 tun watan Nuwamban, 2023
  • Shugabar ma'aikatan jihar, Hannah Odiyo, ta ce an ɗauki wannan matakin ne saboda ma'aikatan sun taka umarnin gwamnati
  • Ta ce gwamnatin Kogi ta tsiri sabunta bayanan ma'aikata ne domin tantance adadinsu da kuma sabun bayanansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin Gwamna Yahaya Bello na APC ta dakatar da biyan albashin ma'aikata 231 da ke aiki a ƙarƙashinta.

Gwamnatin ta ɗauki matakin daina biyan waɗannan ma'aikata albashinsu na wata wata saboda sun gaza bin umarninta na sabunta bayanansu.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.
Gwamnatin Kogi Ta Dakatar da Biyan Ma'aikata Sama da 200 Albashi Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Shugabar hukumar ma'aikatan jihar, Misis Hannah Odiyo, ce ta bayyana haka a Lokoja, babban birnin jihar Kogi ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, 2024.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu da wasu sabbin daraktocin ma'aikatar al'adu sun gana da minista, Hannatu Musawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta faɗi haka ne a wurin kaddamar da fara raba katin shaida (ID Card) ga dukkan ma'aikatan jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Meyasa aka dakatar da albashin ma'aikatan?

Misis Odiyo ta yi bayanin cewa ma’aikatan da wannan matakin ya shafa sun guje wa bin umarnin gwamnatin jihar Kogi na sabunta bayanan su.

Shugabar ma'aikatan ta ce an dakatar da biyan albashin ma’aikatan da abin ya shafa tun watan Nuwamba 2023 har zuwa yau kuma har yanzu babu wanda ya kawo ƙorafi.

Odiyo ta ƙara da cewa an buƙaci kowa ya sake kai bayanansa ne a wani yunkuri na kara tabbatarwa da tantance bayanan ma’aikatan, The Pulse ta ruwaito.

Ta ce a watan Mayun 2022, ofishinta ya aika da takarda (Bio Data Form) ga dukkan ma’aikatu da hukumomi (MDAs) domin ma’aikatan gwamnati su cike su maida.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani 'Bam' ya tashi da mutane a jihar arewa, ya tafka mummunar ɓarna

A kalamanta ta ce:

"Ko da yake aikin ya nuna gazawa da yawa daga cikin MDAs, jimillar ma'aikata 231 ne suka gaza sabunta bayanansu, hakan ya sa aka dakatar da albashin su tun watan Nuwamba 2023 har zuwa yau."

Yan majalisa 16 na cikin matsala a Filato

A wani rahoton kuma Kakakin majalisar dokokin jihar Filato ya yi magana kan rantsar da ƴan majalisar APC 16 da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara.

Gabriel Dewan ya ce ba zai karɓe su ba kuma ba zai yarda korarrun mambobin PDP su sake dawowa majalisar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262