Kano: An Aike da Babban Saƙo Ga Gwamna Abba Kan Kwamishinan Da Ya Yi Wa Alƙalai Barazanar Kisa

Kano: An Aike da Babban Saƙo Ga Gwamna Abba Kan Kwamishinan Da Ya Yi Wa Alƙalai Barazanar Kisa

  • Jigon jam'iyyar APC ya bukaci gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta kama tsohon kwamishinan da ya yi barazanar kashe alƙalai
  • Ɗawisu ya yi wannan kiran ne bayan kama fitaccen ɗan siyasan nan, Abdulmajid Ɗanbilki Kwamanda kan barazanar da ya yi
  • Legit Hausa ta fahimci cewa Kano na ɗaya daga cikin jihohin da siyasarsu ke jan hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Salihu Tanko Yakasai wanda aka fi sani da Ɗawisu ya roƙi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kama tsohon kwamishinan da ya yi barazana ga alƙalan kotun zaɓe.

Dawisu, tsohon mai ba tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje, shawara kan midiya ya buƙaci Gwamna Abba ya kama tsohon kwamishinan nasa kan barazanar kisa ga alƙalan kotu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba, Sule da wasu gwamnoni 7 da suka shirya zartar da hukuncin kisa kan masu garkuwa

Dawisu da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Abdulmajid Kwamanda: An Yi Kira Ga Gwamnan Kano Ya Kama Tsohon Kwamishinansa Hoto: Nifemi Oguntoye, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Me tsohon gwamnan ya faɗa kan alƙalan?

Idan baku manta ba, Adamu Aliyu Kibiya, kwamishinan filaye a wancan loƙacin a watan Satumba, 2023, ya sha alwashin tada zaune tsaye ga mazauna jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, za su rikita Kano fiye da matsalar tsaron da ake fama da shi a jihohin maƙota irinsu Kaduna da Katsina.

Yayin da ake tunanin cewa cin hanci aka bai wa alkalan kotun sauraron kararrakin zabe domin su ba NNPP rashin nasara, Aliyu ya yi wannan katoɓara.

A lokacin ya ce idan har alƙalan suka yanke hukuncin kayar da NNPP, to sun yi ta bakin rayuwarsu. Bayan haka ne gwamnan ya tsige Aliyu.

Hassan Sani Yusuf, babban mai taimakawa Gwamna Abba kan harkokin midiya ya ce gwamnati na maraba da adawa mai tsafta amma banda cin mutunci.

Kalaman Tukur na zuwa ne bayan hukumar yan sandan farin kaya DSS ta kama Abdulmajid Ɗanbilki Kwamanda, bisa kalaman tunzura da ya yi cewa zasu hana zaman lafiya a Kano.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Ɗawisu ya buƙaci Abba ya sa a kama tsohon kwamishinan

Da yake maida martani kan kama Kwamanda a shafinsa na X ranar Talata da yamma, Dawisu, tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PRP, ya rubuta:

"Wannan abin farin ciki ne, muna bukatar zaman lafiya a Kano. Amma ina fata gwamnati za ta kama tsohon kwamishinanta kuma mai ba ta shawara, wanda ya yi barazanar kashe alkalai."

Yan majalisar APC 16 na cikin matsala a Filato

A wani rahoton na daban Kakakin majalisar dokokin jihar Filato ya yi magana kan rantsar da ƴan majalisar APC 16 da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara

Gabriel Dewan ya ce ba zai karɓe su ba kuma ba zai yarda korarrun mambobin PDP su sake dawowa majalisar ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262