2027: Tsohon Hadimin Buhari Ya Bayyana Abun da Dinkewar Kwankwaso da Ganduje Ke Nufi Ga PDP

2027: Tsohon Hadimin Buhari Ya Bayyana Abun da Dinkewar Kwankwaso da Ganduje Ke Nufi Ga PDP

  • Yanayin siyasar Najeriya na shirin daukar sabon salo yayin da jam'iyyun kasar ke zawarcin manyan yan siyasa su dawo cikinsu
  • Kiraye-kirayen da mutane ke yi akan neman Sanata Rabiu Kwankwaso ya dawo APC ya kara karfi a yan baya-bayan nan
  • Sai dai, Bashir Ahmad ya ce sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwaso zai karawa jam'iyya mai mulki a kasar karfi a jihar Kano, tare da kawo babban cikas ga PDP a zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya jajirce a kokarinsa na dinke baraka tsakanin manyan yan siyasar Kano biyu, Abdullahi Ganduje da Rabiu Kwankwaso.

Ganduje dai shine shugaban jam'iyyar APC na kasa yayin da Kwankwaso kuma ke jan ragamar jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

Ni zan zama shugabanka da zarar ka shigo APC, Ganduje ya fadawa Kwankwaso

Bashir Ahmad ya ce dinkewar Kwankwaso da Ganduje zai kawo cikas ga PDP a 2027
2027: Tsohon Hadimin Buhari Ya Bayyana Abun da Dinkewar Kwankwaso da Ganduje Ke Nufi Ga PDP Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR/Facebook@BashirAhmaad/@KwankwasoRM/Twitter
Asali: UGC

Tun bayan kammala shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, wacce a cikinta Kotun Koli ta tabbatar da nasarar dan takarar jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, mutane ke ta hasashen cewa Kwankwaso zai koma APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rade-radin ya kara karfi ne a baya-bayan nan bayan bayyanawa wani hoton Kwankwaso da babban jigon jam'iyyar mai mulki, Bisi Akande.

PDP za ta gamu da gagarumin cikas, Bashir Ahmad

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya shiga sahun masu zawarcin Kwankwaso ya dawo jam'iyyar APC.

Bashir ya bayyana cewa sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje zai kawo gagarumin cikas ga babbar jam'iyyar adawa ta PDP a 2027.

A cewarsa, idan har aka yi nasara yan siyasar biyu suka dinke toh jam'iyya mai mulki za ta dawo da karfinta a jihar Kano.

Ya kuma bayyana cewa dawo da karfin APC a Kano tamkar sun lashe zabe ne a 2027, don zai zama kamar an yi an gama.

Kara karanta wannan

Bayan Sarkin Kano ya yi magana, Lauyoyi Musulmai sun yi babban abu 1 kan sace yaran Arewa zuwa Kudu

Ya bayyana hakan ne a ciki wata wallafa da ya yi a shafinsa na X a ranar Talata, 23 ga watan Janairu.

Ya ce:

"Yiwuwar sulhu tsakanin Sanata Rabi'u Kwankwaso da Dr. Abdullahi Ganduje zai zama gagarumin cikas ga babbar jam'iyyar adawa ta PDP. Idan jam’iyyar mu ta APC ta dawo da karfinta a Kano, za mu iya bayyana cewa an tashi wasan gobe."

Menene ra'ayin Kanawa kan yin sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwaso?

Legit Hausa ta tuntubi wasu mazauna Kano don jin ra'ayinsu game da wannan kira da wasu ke yi na sulhunta tsakanin tsoffin gwamnoninsu, Kwankwaso da Ganduje.

Malam Abdullahi Sanka ya ce:

"Ai sulhu alkhairi ne ko a addininmu na Musulunci, kuma za mu so hakan idan har da alkhairi don ko babu komai an yi zaman aminci tsakanin Ganduje da Kwankwaso a baya.
"Sai dai kuma wannan abu ne mai kamar da wuya kasancewar kowannensu na ganin ya kai kuma ya isa gayya."

Kara karanta wannan

"Ba za ka fadi ba": Ganduje ya shiga Kano da jiniya, Kanawa sun yi maraba da 'uban Abba'

A nasa bangaren Malan Ibrahim cewa ya yi:

"Ai adawa mai karfi ita ce siyasar amma idan manyan ginshikai gaba daya suka taru a waje daya sai a koma yin siyasar jam'iyya daya wacce sam bata da dadin harka.
"Domin yana shugabanni yi wa talakawansu aiki gani suke duk inda aka kai aka komo su din ne za su yi nasara.
"Ba laifi bane idan sun yi sulhu a tsakaninsu amma koma ya zauna a inda yake."

Dattawan APC a Kano sun shawarci Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa dattawan jami'yyar APC a Kano sun kirayi Shugaba Tinubu da ya yi fatali da kiran a kori shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje.

Dattawan har ila yau, sun kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jam'iyyar su watsar da kiran matasan a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng