Kano: Dattawan APC a Jihar Sun Shawarci Tinubu Kan Korar Ganduje, Sun Bayyana Matsayarsu
- Yayin da ake kiraye-kirayen korar shugaban APC, Abdullahi Ganduje, Dattawan jami'yyar sun shawarci Tinubu
- Dattawan sun bukaci Shugaba Tinubu da ya yi watsi da wannan kira inda suka ce daukar nauyinsu aka yi don bata wa Ganduje suna
- Shugaban kungiyar, Abubakar Indabawa da sakatarenta, Musaddiq Wada Waziri sun bayyana cewa ba a san matasan a APC ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dattawan jami'yyar APC a Kano sun kirayi Shugaba Tinubu da ya yi fatali da kiran a kori shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje.
Dattawan har ila yau, sun kuma bukaci masu ruwa da tsaki a jam'iyyar su watsar da kiran matasan a jihar.
Mene dattawan APC ke cewa kan Ganduje?
Hakan ya biyo bayan ganawar gaggawa da dattawan suka yi a yau Litinin 22 ga watan Janairu, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Abubakar Indabawa da sakatarenta, Musaddiq Wada Waziri sun bayyana cewa ba a san matasan a APC ba.
Suka ce kawai daukar nauyinsu aka yi inda suke bayyana kansu a matsayin 'yan jami'yyar APC.
Dattawan suka ce matasan ba 'yan APC ba ne
Sanarwar ta ce:
"Wannan ba matasan jam'iyyar APC ba ne, kawai an dauki nauyinsu ne don kawo cikas a kokarin da Ganduje ya yi wa jam'iyyar.
"Tun bayan hawanshi kujerar watanni bakwai da suka gabata, ya jagoranci sulhu da 'yan jami'yyar a jihohin Rivers da Ondo da sauran jihohi."
Har ila yau, Dattawan sun ce matasan ba su da alaka da jam'iyyar inda suka bukaci jami'an tsaro su bincike su, cewar Independent.
Suka ce mafi yawan masu neman ruguza Ganduje su na jin haushi yafi kowa bai wa Tinubu kuri'u a Arewacin Najeriya a matsayin gwamna.
APC ta magantu kan korar Ganduje
Kun ji cewa, jami'yyar APC a Kano ta yi zazzafan martani kan kirar korar shugabanta, Dakta Abdullahi Ganduje.
Wasu matasan APC ne a jihar suka bukaci Tinubu da ya kori Ganduje daga mukaminsa saboda gaza kawo jihar Kano a zabe.
Asali: Legit.ng