Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Dalilin da Zai Sanya Kwankwaso Ya Yi Nasara a APC

Tsohon Hadimin Buhari Ya Fadi Dalilin da Zai Sanya Kwankwaso Ya Yi Nasara a APC

  • Bashir Ahmad ya yi magana kan yiwuwar sauya sheƙar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabi'u Kwankwaso, zuwa APC
  • Wannan dai na zuwa ne bayan ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, Bisi Akande, ya haɗu da Kwankwaso kwanan nan
  • Tsohon hadimin na Buhari, Bashir Ahmad ya nuna cewa ana maraba da Kwankwaso da mabiyansa a jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Bashir Ahmad, tsohon mataimaki na musamman kan harkokin sadarwa na zamani ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan yiwuwar sauya shekar Rabiu Kwankwaso zuwa APC.

Kwankwaso wanda ya kasance mai riƙe da tutar jam’iyyar NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya zama abin magana a ƙarshen makon nan, bayan an ganshi tare da Bisi Akande, wani gogaggen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya yi martani kan yiwuwar sauya shekar Kwannkwaso zuwa APC

Bashir ya yi martani kan yiwuwar sauya shekar Kwankwaso
Bashir ya ce APC za ta yi maraba da Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Wannan dai na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da wani ɓangare na jam'iyyar NNPP ya tabbatar da cewa korar Kwankwaso na nan daram, kuma akwai wani sabon raɗe-raɗin cewa zai sauya sheƙa zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Bashir ya ce kan yiwuwar sauya sheƙar Kwankwaso?

Da yake mayar da martani kan lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, 21 ga watan Janairu, Bashir Ahmad ya bayyana cewa APC za ta yi murnar karɓar Kwankwaso zuwa cikin jam'iyyar.

Tsohon hadimin ya bayyana cewa Kwankwaso yana da duk abin da ake bukata don yin fice a jam’iyya mai mulki, inda ya ƙara da cewa “siyasa magana ce ta yawan jama'a."

Tsohon hadimin na Buhari ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Za mu yi farin ciki da maraba da Sanata Rabi'u Kwankwaso da mabiyansa zuwa babbar jam'iyyarmu, siyasa wasa ne na yawan jama'a, kuma Kwankwaso ya mallaki adadin da ake buƙata domin ya yi fice a kowane irin fagen siyasa."

Kara karanta wannan

Buhari ya faɗi dalilin da ya sa gwamnatinsa ba ta kashe wani shugaban ƴan ta'adda ba, ta yi masa gata 1

Tinubu Ya Buƙaci Ganduje Ya Sasanta da Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sasanta da Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban ƙasar ya kuma buƙaci Ganduje ya jawo duk wani ra'ayin shiga APC, zuwa cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng