Yayin da Ake Kirar Korar Ganduje, Tsohon Shugaban PDP Ya Watsar da Lema Ya Dawo APC, Ya Fadi Dalili

Yayin da Ake Kirar Korar Ganduje, Tsohon Shugaban PDP Ya Watsar da Lema Ya Dawo APC, Ya Fadi Dalili

  • Yayin da ake kiraye-kirayen korar shugaban APC, Umar Ganduje wani jigo ya dawo jam’iyyar a jihar Ogun
  • Tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Injiniya Bayo Dayo ya watsar da kashin jam’iyyar inda ya koma APC
  • Bayo ya ce ya sauya sheka zuwa jam’iyyyar APC saboda irin ayyukan alkairi da Shugaba Tinubu ke yi a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Injiniya Bayo Dayo ya watsar da jam’iyyar saboda wasu dalilai.

Bayo ya ce ya sauya sheka zuwa jam’iyyyar APC saboda irin ayyukan alkairi da Shugaba Tinubu ke yi a Najeriya.

Tsohon shugaban PDP ya sauya sheka zuwa APC
Tsohon Shugaban PDP, Bayo Dayo Ya Watsar da Lema Ya Dawo APC. Hoto: Ganduje Umar Abdullahi.
Asali: Facebook

Mene dalilin komawar jigon PDP zuwa APC?

Kara karanta wannan

Hotunan Kwankwaso da Akande ya saka shakku kan makomar Sanatan, kujerar Ganduje na cikin matsala

Ya ce ya yi watsi da PDP ne saboda rashin mutuntawa da kuma rashin bin tsarin doka bayan shafe shekaru takwas a kan kujerar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa bayan ayyukan alkairi na Tinubu, Gwamna Abiodun na jihar ya kara masa karfin gwiwar barin jam’iyyar, cewar Tribune.

Dayo ya bayyana haka ne yayin da ya ke bayanin sauya shekar tashi a karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar Ogun.

Da aka tambaye shi dalilin barin PDP, Dayo ya ce ba zai taba ci gaba da zama a jam’iyyar da babu tsari da mutuntawa ba, cewar Vanguard.

Mene martanin jigon PDP?

Ya ce:

“PDP yanzu babu tsari inda za a ce gwamnoni biyar suna zurma kafarsu a ko wace jam’iyya ba tare da taraddadi ba.
“Ba na bukatar kasancewa a cikin irin wannar jam’iyya inda shugabanninta ba sa mutunta kansu.”

Kara karanta wannan

Bai da Amfani: A fatattaki Ganduje, a maido mana da Kwankwaso in ji Matasan APC

Bayo ya ce wannan sauya shekar za ta hada shi da tsoffin wadanda suke tare a siyasa inda ya ce ya san Gwamna Abiodun tun shekarun baya.

APC ta lashe kujerun ciyamomi 27

A wani labarin, jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben dukkan shugabannin kananan hukumomi 27 a jihar Borno.

Har ila yau, jam’iyyar ta kuma lashe zabukan kansiloli 312 da aka gudanar a jihar da suke wakiltar unguwanni.

An gudanar da zaben ne a ranar Asabar 20 ga watan Janairu yayin da mace ta farko ta samu nasara a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.