Ministan Tinubu Ya Nuna Gwamnan Arewa 1, Ya Bayyana Ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Ministan Tinubu Ya Nuna Gwamnan Arewa 1, Ya Bayyana Ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

  • Ministan tsaro, Muhammad Badaru, ya yabawa magajinsa na jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi bisa ayyukan da ya faro
  • Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya ce a yanzu mutane sun gane gaskiyar abin da ya faɗa musu game da Ɗanmodi a lokacin kamfe
  • Ya faɗi haka a ziyarar ya kai jihar wanda ake kyautata zaton ita ce ta farko tun bayan sauka daga mulki a watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru, ya ce ayyukan ci gaban da Gwamna Umar Namadi ya kinkimo ya ƙara wanke shi daga nuna shi a matsayin magajinsa.

Badaru, wanda yanzu shi ne ministan tsaron Najeriya, ya ziyarci Jigawa ne ranar Asabar, ana zaton ita ce ziyararsa ta farko tun bayan da ya bar mulki a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Badaru ya yabi Ɗanmodi.
Na Wanke Kaina Kan Zabin Wanda Ya Gaje Ni, Tsohon Gwamnan Jigawa Hoto: Buhari Hussaini
Asali: Facebook

A rahoton Premium Times, Badaru ya aza harsashin gina gidaje masu tarin yawa na jihar a Panisau, wani yanki da ke bayan garin Dutse, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wurin taron, tsohon gwamnan ya ce:

"Na yi farin ciki da ci gaban da aka samu zuwa yanzu. Na ga mutane a cikin farin ciki da murmushi kuma suna gaya mani cewa na bar wani adalin shugaba wanda ke ƙoƙarin sauke nauyi.
“Na gaya muku a lokacin kamfe, shi mutum ne mai gaskiya ne da himma sosai. Allah ya kubutar dani duba da ci gaban da ake samu a jihar nan, na tabbata zai yi abin da ni kaina ban yi muku ba.
"Ina ƙara gode muku da kuka bamu amanarku, mun bar jihar Jigawa cikin yanayi mai kyau kuma jagoran da ke jan ragamar mulki a yanzu zai yi abinda ya dace."

Kara karanta wannan

Kakakin majalisar dokoki ya aike da saƙo na musamman kan nasarar gwamnan arewa a Kotun Ƙoli

Namadi ya fara aiki ba kama hannun yaro

Babban aikin gina gidajen da Gwamna Namadi ya ɗauko ya kunshi gidaje 1,500, wanda za a gina a fadin jihar, inda babban birnin jihar Dutse ke da guda 600.

Gwamna Umar Namadi, ya ce gwamnatin jihar karkashin jagorancinsa ce za ta dauki nauyin biyan kuɗin aikin gina gidajen.

Ya ce za a gina su a hedkwatar masarautu biyar da wasu garuruwa uku, sune, Dutse, Ringim, Hadejia, Gumel, Kazaure, Kafin Hausa, Birnin Kudu da kuma Babura.

Aminu Maje, mazaunin Birnin Kudu a Jigawa ya ce babu tantama Gwamna Ɗanmodi mutumin kirki ne kuma yana yi wa jihar aiki tun daga hawansa mulki.

Da yake hira da Legit Hausa, Aminu ya ce gwamnan ya yi abubuwan da suka sa mutane suka ƙara kaunarsa, harda waɗanda ba su zaɓe shi ba.

Ya ce:

"Ɗanmodi mutumin kirki ne, ɗaya daga cikin abinda ya yi ya ƙara shiga ran jama'a shi ne ɗaukar malaman lafiya aiki, sun jima suna aiki ana ɗan ba su wani abu."

Kara karanta wannan

Ana jita-jitar Kwankwaso zai sauya sheƙa, wani gwamna ya gana da jiga-jigan APC, ya buƙaci abu 2

"Ni dai ina ganin ya ɗauko hanyar kara inganta jihar Jigawa kuma muna masa fatan alheri."

Yan Bindiga Sun Sako Karin Mutanen Abuja

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun saƙo karin mazauna birnin tarayya Abuja da suka yi garkuwa da su tun ranar Lahadin da ta wuce.

Tun farko mahara sun yi awon gaba da mutum 10 yayin da suka kai hari Sagwari Estate a karamar hukumar Bwari, sun kashe 3 daga ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262