Kano: Bayan Rashin Nasara a Kotun Koli, Ganduje Ya Sake Shirya Wargaza Shirin NNPP a Zabe Mai Zuwa
- Jam’iyyar APC a jihar Kano ta yi wata muhimmiyar ganawa don sake shirin kwace mulki a zabe mai zuwa
- Jam’iyyar ta dauki matakin ne yayin wata ganawa a ranar Juma’a 19 ga watan Janairu don sake duba yanayin shari’ar zaben
- Wannan na zuwa ne bayan ta shan kaye a shari’ar zaben jihar da Kotun Koli ta bai wa Abba Kabir nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Bayan shan kaye a Kotun Koli, jam’iyyar APC a jihar Kano ta sake shiri don tunkarar zaben da ke gaba.
Jam’iyyar ta dauki matakin ne yayin wata ganawa a ranar Juma’a 19 ga watan Janairu don sake duba yanayin shari’ar zaben.
Mene dalilin ganawar ta APC a Kano?
Sannan za a sake gagarumar ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a jihar daga kananan hukumomi 44 a ranar Alhamis 25 ga watan Janairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar wanda shugaban jam’iyyar a Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta ya godewa Tinubu kan inganta jam’iyyar a jihar da Najeriya.
An yi ganawar ce don inganta fahimtar juna a tsakanin ‘yan jam’iyyar da samo hanyar samun nasara a zabuka masu zuwa, cewar The Nation.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa ya sanya wa hannu ta hadin gwiwa.
Manyan bakin da suka halarci ganawar
Sanarwar ta ce:
“Wannan ganawa ta nuna godiya ce ga Shugaba Tinubu ganin yadda ya ke nuna kauna ga jihar Kano da kuma jam’iyyar APC.
“Sannan ta godewa shugaban kan irin hobbasa da ya ke yi don ganin jam’iyyar ta ci gaba a jihar dama kasa baki daya.
“Har ila yau, jam’iyyar na maraba ga dukkan masu son sauya sheka zuwa APC don ba da ta su gudunmawa.”
Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai mataimakin Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau da kuma dan takarar jam’iyyar a jihar, Nasiru Gawuna da mataimakinsa, Murtala Sule Garo.
Sauran sun hada da karamar Minsitar Abuja, Dakta Mariya Bunkure da Ministan Gidaje, Injiniya Abdullahi Gwarzo, cewar Leadership.
Sarkin Kano zai kaddamar da aiki
A wani labarin, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero zai kaddamar da gagarumin aiki a jihar Kano.
Sarkin zai kaddamar da bude sabon asibiti don inganta lafiya a jihar musamman ga marasa karfi.
Asali: Legit.ng