Bayan Sha da Kyar a Kotu, Gwamnan PDP Ya Bugi Kirji Bayan Nasara a Shari'o'i 38 a Zabe, Akwai Dalili
- Yayin da yi nasara a Kotun Koli, Gwamna Sheriff na jihar Delta ya bugi kirji da irin nasarorin da ya samu
- Oborevwori ya ce ya yi nasara a shari'o'i 38 tun zabe fidda gwani har zuwa yanzu kuma duk ya yi nasara
- Wannan na zuwa ne yayin da Kotun Koli ta tabbatar da nasarar gwamnan a jiya Juma'a 19 ga watan Janairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya ce ya yi nasara a shari'o'i 38 kuma duk ya yi nasara.
Sheriff ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 19 ga watan Janairu bayan ya samu nasara a Kotun Koli.
Mene Gwamna Sheriff ke cewa?
Oborevwori ya ce wadannan nasarorin ya same su ne tun daga zaben fidda gwani har zuwa babban zabe da kuma nasarar da ya samu a Kotun Koli.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci wadanda suka yi rashin nasara da sauran 'yan adawa da su zo a hada kai don gina Delta baki daya, cewar The Nation.
Ya ce:
"Wannan nasara ce ga mutanen mu, wanda ya nuna ubangiji ya na tare da mu kuma shi kadai zai mana haka.
"Wannan nasara ta mu ce kuma ina yi wa 'yan Delta alkawari zan zama gwamnan Delta ga kowa."
Sheriff ya ce Ubangiji ne ya kaddara zai ya zama gwamnan jihar inda ya godewa 'yan jihar game da goyon baya da suke ba shi.
Ya bugi kirji kan nasarorin da ya samu
Ya kara da cewa:
"Wannan nasara ita ce ta 38 tun kafin zaben zabe wanda duk na yi nasara.
"Ko gwamnan da ya yi shekaru takwas bai fuskanci irin wannan shari'o'i ba."
Wannan na zuwa ne bayan Kotun Koli ta tabbatar da nasarar gwamnan a shari'ar zaben jihar, cewar The Guardian.
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff
A wani labarin, Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Delta da ake takaddama a kai.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Sheriff Oborevwori na jami'yyar PDP a matsayin zababben gwamna.
Har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar APC, Omo-Agege saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng