Gwamnan APC Ya Bayyana Muhimmin Abu 1 da Ya Kamata Dan Takarar PDP Ya Yi Bayan Hukuncin Kotun Koli
- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yaba wa abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan
- Gwamnan ya yaba da jajircewarsa wajen tunkarar ɓangaren shari'a har zuwa Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan jihar
- Uba Sani ya yi kira a gare shi da ya zo su haɗa hannu domin ciyar da jihar gaba bayan Kotun Ƙoli ta tabbatar da nasararsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya jinjina wa abokin takararsa, Isa Ashiru, na jam’iyyar PDP, biyo bayan kammala shari'ar zaɓen gwamnan jihar a ranar Juma'a, 19 ga watan Janairu.
A hukuncin da ta yanke kan rikicin gwamnan jihar Kaduna a ranar Juma’a, Kotun Ƙoli ta amince da nasarar Uba Sani, a zaɓen gwamnan jihar na ranar, 18 ga watan Maris, 2023.
Kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙolin ƙarkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ya bayyana cewa ƙarar da Ashiru ya shigar ba ta da wani inganci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana a shirin 'Politics Today' na gidan Talabijin na Channels tv, sa'o'i kaɗan bayan yanke hukunci, gwamnan ya ce matakin da ɗan takarar PDP ya ɗauka, ya ƙara zurfafa dimokuraɗiyya da bin doka da oda.
A kalamansa:
"Ina so in yi amfani da wannan damar domin in gode wa ɗan uwana kuma abokina, Isah Ashiru, aƙalla bisa yadda ya rungumi tsarin shari’a tare da huce fushinsa ta hanyar zuwa Kotun Ƙoli a wannan mawuyacin lokaci.
"Idan kun tuna, ya je kotun zaɓe, bayan kotun zaɓe ya garzaya zuwa kotun ɗaukaka ƙara, bayan kotun ɗaukaka ƙara a yanzu Kotun Koli. A gare ni, abin da ya yi abin yabawa ne. Tsarin dimokuraɗiyya ne.
"Idan baka gamsu ba, ka tunkari ɓangaren shari’a. Tabbas abin da ya yi ke nan. A yau ya tabbata, cewa Kotun Koli ta amince da zaɓe na gaba ɗaya. Tabbas, wannan hukuncin ya yi kyau sosai."
Wane kira Uba Sani ya yi wa Isa Ashiru?
Gwamnan ya yi kira ga ɗan takarar jam’iyyar PDP da ya haɗa kai da gwamnatinsa domin kai jihar Kaduna zuwa ga tudun mun tsira.
A kalamansa:
"Yanzu da Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen, ina so in yi kira ga Isah Ashiru da ya ba ni haɗin kai domin ciyar da jihar Kaduna gaba.
"Don haka ne nake so in gayyace shi da duk wani ɗan jihar Kaduna da ke da abin da zai iya bayar wa, mu yi aiki tare bisa tsarin dimokuradiyya."
Legit Hausa ta tuntuɓi Zahraddeen Abubakar wani ɗan jam'iyyar APC a jihar Ƙaduna wanda ya nuna farin cikinsa kan nasarar da gwamnan ya samu a Kotun Ƙoli.
Ya bayyana hukuncin a matsayin babbar nasara ga al'ummar jihar Kaduna.
A kalamansa:
"Nasara ce mai muhimmanci a wajen ƴan jihar Kaduna saboda hukuncin Kotun Ƙoli ba komai bane illa tabbatar da zaɓin kaso mafi yawa na mutanen jihar Kaduna.
"Sannan mutanen jihar Kaduna suna neman wanda dama zai cigaba da ayyukan alkhairi ne wanda tsohon Gwamna Malam Nasir El- Rufai ya fara ba wai a dawo baya ba a fara daga farko ba."
Gwamna Sule Ya Shawarci Ombugadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya shawarci David Ombugadu na jam'iyyar PDP.
Gwamnan ya shawarci Ombugadu da ya jira lokacinsa ya yi domin zama gwamnan jihar Nasarawa.
Asali: Legit.ng