Kano: Ko Yanzu Sun Shiga Taitayinsu, Kwankwaso Ya Bugi Kirji da Yawan Jama’a a Zabe
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana yadda suka nuna wa duniya yawan jama’a
- Kwankwaso ya ce ko ba komai su ba kowa ba ne amma sun tabbatarwa duniya cewa suna da jama’a
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabri ya samu nasara a Kotun Koli a ranar Juma’a da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Sanata Rabiu Kwankwaso a sake martani bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli.
Kwankwaso ya ce ko yanzu sun nuna wa duniya cewa suna da jama’a wanda hakan ya yi tasiri a nasararsu.
Mene Kwankwaso ke cewa a Kano?
Sanata Kwankwaso ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sadarwa.
Bayan sha da kyar a kotu, Gwamnan PDP ya bugi kirji bayan nasara a shari'o'i 38 kan zabe, akwai dalili
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce su a ‘yan siyasa ba alkalai ba ne kuma ba sojoji ko ‘yan sanda ba amma sun nuna wa duniya jama’a nasu ne.
Ya kara da cewa ko a 2003 akwai damar da za su kwace amma suka bari duk da sun sani an musu rashin adalci.
Hakurin da suka yi shekarar 2003?
Ya ce:
“Mu a ‘yan siyasa alkalai ne? mu sojoji ne? mu ‘yan sanda ko INEC ne?, amma dai mun nuna wa duniya cewar jama’ar dai namu ne.
“Ko a 2003 da aka zo rigingimu, muna da damar da za a yi irin wadannan abubuwa na kwata, tabbas ba a yi amana adalci ba amma mun yi hakuri.”
Sanatan ya ce haka su ka yi hakuri abin ya wuce da haka saboda a zauna lafiya har wasu suke cewa gwara ma da Allah ya saka suka fadi saboda damar da suka samu daga baya.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya yi nasara a Kotun Koli a ranar Juma’a 12 ga watan Janairu.
Kwankwaso ya magantu kan masarautun Kano
A wani labarin, Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi magana kan halin da ake ciki game da masarautun Kano.
Kwankwaso ya ce tabbas dole za a zo ayi zama kan wadannan masarautun ganin yadda aka kirkire su.
Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya kirkiro masarautun a jihar.
Asali: Legit.ng