Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Nasarawa Bayan Hukuncin Kotun Koli Kan Nasarar Gwamna Sule
- Zanga-zanga ta ɓalle a Lafiya babban birnin jihar Nasarawa biyo bayan nasarar Gwamna Abdullahi Sule a Kotun Ƙoli
- Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar sun toshe titin Lafia zuwa Jos, lamarin da ya tilastawa matafiya canza hanya
- Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan kotun koli ta yanke hukunci kan taƙaddamar zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lafia, jihar Nasarawa - Rahotanni sun nuna cewa zanga-zanga ta ɓarke a Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan zaben gwamna.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.
An toshe hanyar Lafia zuwa Jos gaba daya yayin da masu zanga-zangar suka kunna wuta don hana matafiya da sauran masu amfani da hanyar wucewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wakilin jaridar Daily Trust, wanda ya je wurin zanga-zangar ya tattaro cewa lamarin ya tilasta wa masu ababen hawa bin wasu hanyoyi na daban da za su ratsa su wuce Lafia.
Wani makanikin mota mai suna, Mallam Dogo Audu, ya yi kira da a kara tura jami’an tsaro domin kwantar da wannan tarzoma da tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Rahoton Channels tv ya tattaro cewa zuwa yanzu jami'an tsaro sun isa wurin kuma sun fara ƙoƙarin kwantar da hankalu da daƙile yaɗuwar wannan tashin hankali.
Shaguna da wuraren kasuwanci da suka hada da makarantu a cikin birnin Lafia sun rufe ba zato ba tsammani don guje wa abin da ka iya zuwa ya komo.
Emefiele ya musanta tuhuma 20 da ake masa
A wani rahoton na daban kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya musanta dukkan tuhume-tuhume 20 da aka shigar kansa a gaban kotu.
Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ƙara yawan tuhume-tuhumen da take wa Emefiele, ta miƙa wa Kotu.
Asali: Legit.ng