Kotun Koli Ta Yi Hukuncin Karshe a Shari'ar Neman Tumbuke Gwamnan Gombe, Ta Fadi Dalillai
- Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan jihar Gombe a Najeriya
- Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamna
- Kotun kuma har ila yau, ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Jibrin Barde saboda rashin hujjoji
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan jihar.
Wane hukunci kotun ta yanke a zaben Gombe?
Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP, Muhammad Jibrin Barde saboda rashin gamsassun hujjoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin hukuncin, jagoran alkalan guda biyar, Mai Shari'a, Kudirat Kekere-Ekun ta yi watsi da korafe-korafen Jibrin Barde kamar yadda Kotun Daukaka Kara ta yi.
Ta ce korafe-korafen da dan takarar PDP ya gabatar a gaban kotun ba su da tushe bare makama da za a yi amfani da su, cewar TheCable.
A baya, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya na APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
Martanin kotun kan korafe-korafen PDP
Yayin da kuma ta yi watsi da karar Jibrin Barde wanda ya yi takara a jam'iyyar PDP a zaben na watan Maris, cewar The Nation.
Tun farko, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya lashe zaben.
Dan Barde a bangarensa, ya kalubalanci zaben da aka gudanar a watan Maris da cewa akwai kura-kurai cike a ciki.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauraran shari'ar zabukan jihohi da dama a Kotun Koli da ke Abuja.
Kotun Koli ta yi hukunci a zaben jihar Kebbi
Kun ji cewa Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kebbi a yau Juma'a.
Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Yayin da ta yi watsi da korafe-korafen dan takarar jam'iyyar PDP a zaben, Aminu Bande saboda rashin gamsassun hujjoji.
Asali: Legit.ng