Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci Kan Zabukan Gwamnonin Nasarawa, Kebbi, Gombe Da Wasu
A yau Juma'a 19 ga watan Janairu ne aka sa ran Kotun Koli za ta yanke hukunci kan shari'a zabukan gwamnoni da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Jihohin da za a yanke hukunci kan daukaka kara dangane da shari'arsu sun hada a Nasarawa, Kebbi, Gombe, Ogun da Delta.
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Nasir Idris a matsayin gwamnan Kebbi
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Nasir Idris na APC a matsayin gwamnan Kebbi.
Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka karar da Bande Aminu na PDP ya shigar.
Mai Shari'a Uwani Abba-Aji, wacce ta karanto hukuncin, ta ce ba shi da inganci.
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Yahaya a matsayin gwamnan Gombe
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Muhammad Inuwa na APC a matsayin gwamnan Gombe.
Kotun Kolin ta yi watsi da daukaka karar da Jibrin Mohammed Barde ya shigar.
Mai Shari'a Kekere-Ekun ta ce wadanda suka daukaka karar sun gaza nunawa kotun cewa hukuncin da kotun zabe da kotun daukaka kara suka yi ba dai-dai bane.
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nasarawa
Kotun Kolin ta tabbatar da zaben Abdullahi Sule na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar Nasarawa.
Kotun ta yi fatali da daukaka kara hudu da dan takarar PDP, Emmanuel David Ombugadu, saboda rashin inganci.
Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun, wacce ta karanto hukuncin, ta warware dukkan matsalolin da aka gabatar kan PDP da Ombugadu kuma ta yi watsi da karar.
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Abiodun a matsayin gwamnan Ogun
Kotun Koli ta tabbatar da zaben Dapo Abiodun a matsayin gwamnan jihar Ogun.
Alkalai biyar na kotun, a hukuncin da suka yi tarayya a kai, sunyi watsi da daukaka karar da Oladipupo Adebutu, dan takarar PDP a zaben karshe na gwamna a jihar Ogun.
Da ya ke karanto hukuncin, Mai Shari'a Tijjani Abubakar ya ce Adebutu da jam'iyyarsa sun gaza gabatar da gamsassun hujoji.
Mai sharia Abubakar ya warware dukkan matsalolin da masu daukaka karar suka gabatar, yana mai cewa babu wani nagarta a daukaka karar.
Kotun Koli ta tabbatar da Sheriff Oborevwori a matsayin halastaccen Gwamnan Delta
Kotun Kolin ta tabbatar da zaben Sheriff Oborevwori a matsayin halastaccen gwamnan jihar Delta.
Kotun Koli ayyana halan ne bayan yin watsi da daukaka karar da jam'iyyun APC, SDP da Labour suka shigar.
Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar LP kan gwamnan Delta
Kotun Kolin kuma ta yi fatali da daukaka karar da jam'iyyar Labour da dan takararta a zaben da ya gabata a jihar Delta, Kennedy Pela, na neman soke zaben Gwamna Oborevwori.
Kotun ta warware dukkan matsaloli shida tana mai cewa sun gaza gamsar da kotun cewa an yi ba dai-dai ba.
Jihar Delta: Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar Omo-Agege kan Oborevwori
Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan 2023 a jihar Delta, Ovie Omo-Agege.
Omo-Agege ya nemi kotu ta kwace kujerar Gwamna Sheriff Oborevwori na jam'iyyar PDP.
A hukuncin da aka yanke a yau, tawagar alkalai biyar na Kotun Kolin ta ce Omo-Agege da jam'iyyarsa sun gaza gabatar da gamsassun hujojji cewa ba a bi ka'idojin Dokar Zabe ba.
Gwamnan Nasarawa da magabatansa biyu sun iso Kotun Koli
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa da magabatansa biyu sun iso Kotun Koli.
Magabatan Gwamna Sule da suka zo kotun sune Abdullahi Adamu da Umaru Tanko AlMakura.
Kotun Koli: Gwamnonin da za su san makomansu a yau
Abdullahi Sule (Nasarawa)
Nasir Idris (Kebbi)
Inuwa Yahaya (Gombe)
Sheriff Oborevwori (Delta)
Dapo Abiodun (Ogun)
Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164
Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.