El-Rufai Ne Silar Daukaka Ta, Abbas Ya Fadi Karin Mutum 1 da Ba Zai Manta da Shi Ba
- Kakakin Majalisar Tarayya, Abbas Tajudden ya bayyana wadanda suka masa silar samun kujerar
- Abbas ya ce ba zai taba mantawa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai ba da irin goyon bayansa
- Kakakin Majalisar ya bayyana haka ne a daren jiya Laraba 17 ga watan Janairu yayin karbar bakwancin Gwamna Uba Sani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Hon. Abbas Tajudden ya bayyana manyan mutane biyu da suka taimake shi.
Abbas ya ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da kuma Gwamna Uba Sani a jihar su suka kara masa karfin gwiwa a neman kujerar.
Mene Abbas ke cewa kan El-Rufai?
Ya ce tabbas wadannan mutane biyu sun ba shi dukkan goyon baya tun bayan shiga Majalisar shekaru kadan da suka wuce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin Majalisar ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin Gwamna Uba Sani da Ministan Muhalli, Balarabe Lawal.
Mai magana da yawun kakakin Majalisar, Musa Krishi shi ya bayyana haka a daren jiya Laraba 17 ga watan Janairu, cewar Leadership.
Ya ce:
“Tabbas abin farin ciki ne a farkon wannan shekara ta 2024, mun karbi bakwancin manyan baki daga jiha ta.
“Ina matukar farin ciki da wannan ziyara har zuwa ofishi na, tabbas ba zan taba mantawa da hakan ba.
“Mutane za su yi mamaki idan na ce gwamna na da kuma Minista sun yi matukar ba ni goyon baya tun daga farko.”
Wane sakon godiya Abbas ya tura?
Ya ce ya na godiya da irin goyon bayan da suka ba shi kuma su ke ci gaba da ba shi har zuwa yanzu,The Times ta tattaro.
Ya kara da cewa:
“Za ku sha mamaki cewa duk wannan tsari na neman kujerar kakakin Majalisa ya fara ne daga mutanen nan biyu musamman yaya na Mallam Nasir El-Rufai.
“Mutane da dama za su yi mamaki saboda ana cewa gwamna baya son kakakin Majalisa ya fito daga jiharsa.”
Uba Sani da gwamnonin da za a yanke hukunci
A wani labarin, Gwamna Uba Sani na daga cikin wadanda da suke dakon shari'ar zaben jihohinsu.
A ranar 12 ga watan Janairu ce Kotun Koli ta yanke hukunci a shari'ar zaben jihohi 8 a Najeriya.
Asali: Legit.ng