Abin Ya Yi Wa Ganduje Yawa Bayan Rasa Kano, Ya Na Fuskantar Barazanar Kotu Kan Zaben Jihar APC
- Shugaban jam'iyyar APC, Abdulllahi Ganduje na ci gaba da samun matsin lamba kan zaben fidda gwani a jihar Ondo
- 'Yan takara da suka fafata a zaben sun bukaci a dauki matakin kafin lamarin ya kai ga zuwa kotu
- Wannan na zuwa ne bayan daya daga cikin 'yan takarar, Olugbenga Araoyinbo ya bukaci jami'yyar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Rikicin jami'yyar APC ya kara munana bayan zaben fidda gwani a jihar Ondo, Daily Trust ta tattaro.
Wannan na zuwa ne bayan daya daga cikin 'yan takarar, Olugbenga Araoyinbo ya bukaci jami'yyar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Mene dalilin rikicin a zaben fidda gwanin a Ondo?
An gudanar da zaben fidda gwanin ne a mazabar Akoko da ke Majalisar Tarayya a jihar don maye gurbin wanda ya bar kujerar don mukamin Minista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan kammala zaben da ke cike da hayaniya, dan tsohon babban Sifetan 'yan sanda, Ifeoluwa Ehindero shi ya yi nasara a zaben.
Ehindero ya samu kuri'u 105 daga cikin 106 da aka kada a zaben fidda gwanin wanda ake shirin gudanar da zabe a ranar 3 ga watan Faburairu.
Wace barazana Ganduje ke fuskanta kan zaben?
Ganin yadda aka gudanar da zaben cikin rashin tsari, Araoyinbo ya kalubalanci shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje inda ya ce an gudanar da zaben ba a kan tsari ba.
A cikin takardar korafi da ya fitar, ya bukaci a sake gudanar da zaben ganin yadda aka saba tsarin dokar jami'yyar, cewar Daily Post.
Ya bukaci Ganduje da ya saurari korafe-korafensa don daukar mataki kada abin ya kai ga maka Ehindero a kotu kan zaben.
An samu hatsaniya a zaben fidda gwanin Ondo
A wani labarin, dan tsohon Babban Sifetan 'yan sanda, Sunday Ehindero ya samu nasara a zaben fidda gwani a jihar.
Ifeoluwa Ehindero shi ya lashe zaben fidda gwanin da aka gudanar don maye kujerar dan Majalisa a mazabar Akoko da ke jihar.
Asali: Legit.ng