Ayi Hakuri: Dalilin Neman Afuwar ‘Yan Najeriya Kan Wahalar da Na Jefa Su Inji Buhari
- Muhammadu Buhari ya bude baki ya yi bayani a kan abubuwan da suka faru a lokacin yana mulki
- Tsohon shugaban kasar ya ce dole wasu tsare-tsaren gwamnati suyi sanadiyyar shan wahalar wasu
- Duk abubuwan da suka faru a mulkinsa, Buhari ya tabbatar da cewa ba domin cutar da wani aka yi ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Watanni bakwai da yin ban kwana da karagar mulki, Muhammadu Buhari, ya fito ya yi magana a game da gwamnatinsa.
Mai girma Muhammadu Buhari ya yarda ya kawo wasu tsare-tsare da suka wahalar da al’umma, Premium Times ta kawo labarin.
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce halin da aka shiga ne ya jawo dole ya ba jama’a hakuri daf da barin kujerar mulki a Aso Villa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Buhari bai so a wahala ba
Duk da yadda abubuwa suka kasance, Muhammadu Buhari ya ce sam bai yi haka saboda mutanen kasar su tagayyara a mulkinsa ba.
A jawabinsa wajen kaddamar da littafin aka rubuta a kan shi, Buhari ya ce tsare-tsaren shugabanni su kan jawo wasu su sha wuya.
Buhari ya roki ayi hakura da shugabanni
The Nation ta ce tsohon shugaban kasar ya yi kira ga jama’a su zama masu hakuri da jagororinsu har gwamnati ta iya cin ma nasara.
"Shiyasa na ba irin wadannan mutane hakuri a karshen wa’adinmu a ofis."
"Har yanzu ana cigaba da yin hakuri kuma zai cigaba da zama cikin rayuwarmu ta yau da kullum da cigaban kasa."
"Gwamnati za ta cigaba da neman fahimta da neman goyon al’ummar da ta ke jagoranta har a cin ma matsaya."
- Muhammadu Buhari
Buhari ya ji dadin rubuta tarihin mulkinsa
Buhari wanda ya yi mulki na shekaru takwas ya ji dadin yadda Femi Adesina da Udu Yakubu suka rubuta littafi game da lokacin mulkinsa.
Tsohon shugaban kasar ya ce mutane suna da saurin mantuwa saboda haka littatafan za su taimaka wajen adana tarihin 2015-2023.
Femi Adesina ya fadi makiyan Buhari
An ji labari Femi Adesina wanda shi ne mai magana da yawun Muhammadu Buhari ya fadi manyan makiyan tsohon shugaban Najeriya.
Adesina ya bayyana cewa Buhari ya ci karo da wasu manyan makiya da yake mulki, daga cikinsu akwai wadanda yake zagaye da su a ofis.
Asali: Legit.ng