Tsohon Shugaba Muhammadu Buhari Ya Bayyana Matsayarsa Kan Mulki Tinubu da APC a Taron Abuja
- Muhammadu Buhari ya jaddada cewa har yanzun yana nan tare da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC
- Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wurin taron kaddamar da littafi biyu kan shekarunsa 8 a mulki wanda hadiminsa ya rubuta
- Tinubu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da wasu manyan kusoshi a kasar nan sun samu halarta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa yana nan tare da jagorancin shugaban kasa, Bola Tinubu, da jam’iyyarsa All Progressives Congress (APC).
Buhari ya jaddada cewa yana goyon bayan gwamnatin APC mai ci ne a wurin taron kaddamar da litattafai biyu ranar Talata, 16 ga watan Janairu, 2024.
Litattafan biyu, "Working with Buhari,” da kuma “Muhammadu Buhari: The Nigerian Legacy – 2015 – 2023 (Vols 1-5)," sun maida hankali kan mulkin Buhari na shekaru 8.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ne ya rubuta littafin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Adesina ne ya rubuta littafin, "Working With Buhari" watau aiki da Buhari amma Shola Oshunkeye, tsohuwar ƴar jarida da ta lashe lambar ƙwazo a CNN ta duba shi.
Buhari ya yi magana kan gwamnatin Tinubu
Da yake jawabi a wurin kaddamar da littafan biyu, Muhammadu Buhari, ya ce yana goyon bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC.
Buhari ya ce:
"Ina nan tare da jam'iyyar mu ta APC da gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu."
Manyan ƙusoshin da aka hanga a wurin taron sun haɗa da shugaba Tinubu da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo. Vanguard ta ruwaito.
Bugu da ƙari, tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Yakubu Gowon, da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Abubakar Sirika, sun halarci taron yau Talata.
APC ta fara yunkurin kwato jihar Edo daga hannun PDP
A wani rahoton na daban Tsohon shugaban APC ya bayyana aniyarsu ta sake kwato jihar Edo daga hannun PDP a zaben gwamna mai zuwa a watan Satumba.
Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar ya ce dukkan masu ruwa da tsakin Edo sun maida hankali wajen yadda za a samu nasara.
Asali: Legit.ng