Bwala: Hadimin Atiku Ya Faɗi Abu 1 da Zai Yi Idan Shugaba Tinubu Ya Naɗa Shi Muƙami a Gwamnati
- Duk da sukar da yake sha, Daniel Bwala ya tsaya kan bakarsa cewa a shirye yake ya bai wa gwamnatin Shugaba Tinubu gudummuwa
- Bwala, jigon PDP ya yi ƙarin haske kan ziyarar da aka ga ya kaiwa Bola Tinubu a Villa da kuma yiwuwar ba shi muƙamin gwamnati
- Tsohon kakakin kamfen Atiku Abubakar ya ƙara jaddada cewa goyon bayansa ga Muhammadu Buhari na shekara takwas bai sa ya samu muƙami ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Daniel Bwala, ya nuna sha'awar yin aiki a gwamnati mai ci.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Bwala ke shan suka da caccaka daga wasu ƴan Najeriya sakamakon ziyarar da ya kai fadar shugaban ƙasa ranar 10 ga watan Janairu.
Duk da caccakar da ake masa, Mista Bwala ya bayyana cewa zai ji daɗi idan aka ba shi muƙamin da zai taimaka wajen cika ajendar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bwala, jigo a jam'iyar PDP ya yi wannan furucin ne yayin wata hira a gidan talabijin na Channels cikin shirin 'siyasa a yau' ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu.
Hadimin Atiku zai iya karɓan muƙami daga Tinubu
A kalamansa, tsohon hadimin Atiku ya ce:
"Bari na gaya muku wani abu, idan shugaban kasa ya mun tayin mukamin da nake ganin zai taimaka wajen ci gaban ajandarsa domin na ce zan goyi bayan aiwatar da ajendarsa zan karɓa.
"Zan gode masa na yaba masa fiye da komai amma fa ku sani ba wai muƙamin nake nema ba shiyasa na ce zan mara masa baya.
"Shiyasa nake faɗa maku cewa shekaru takwas da na shafe ina tare da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ban riƙe kowane muƙami ba."
Wannan na zuwa ne kasa da mako ɗaya bayan Bwala ya ce zai goyi bayan Bola Tinubu ko da kuwa hakan zai buƙaci ya koma APC.
Gwamna Fubara ya yi nasara a kotu
A wani rahoton na daban Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya samu nasara a ɗaya daga cikin ƙarrakin da aka ƙalubalanci nasararsa a kotu.
Ƙotun kolin Najeriya ta kori ƙarar jam'iyyar APM da ɗan takararta a zaman ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024.
Asali: Legit.ng