Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Ƙarar da Aka Nemi Tsige Gwamnan PDP Daga Mulki

Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Ƙarar da Aka Nemi Tsige Gwamnan PDP Daga Mulki

  • Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya samu nasara a ɗaya daga cikin ƙarrakin da aka ƙalubalanci nasararsa a kotu
  • Ƙotun kolin Najeriya ta kori ƙarar jam'iyyar APM da ɗan takararta a zaman ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024
  • Hakan ya biyo bayan bukatar janye karar da lauyan APM da Innocent Kere, ya shigar, kuma kotun ta tanadi hukunci a ƙarar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta kawo ƙarshen ƙarar da jam'iyyar Allied People Movement (APM) ta ƙalubalanci nasarar gwamnan jihar Ribas, Simanalayi Fubara.

A zaman ci gaba da sauraron ƙarar ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, 2024 kotun mai daraja ta daya a Najeriya ta ƙori ƙarar APM da ɗan takararta na gwamna, Innocent Kere.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shirya liyafa bayan nasara a kotun koli, ya aike da muhimmin saƙo ga Bola Tinubu

Gwamna Siminalayi Fubara.
Kotun Koli Ta Kori Ƙarar da Jam'iyyar APM Ta Nemi Tsige Gwamna Fubara na Rivers Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Kwamitin alkalai 5 karƙashin jagorancin mai shari'a, Kudirat Kekere-Ekun, ne ya yanke hukunci kan wannan ƙara da aka ɗaukaka zuwa gaban kotun ƙoli, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, Lauyan jam'iyyar APM da ɗan takararta na gwamna a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023 ne ya miƙa bukatar janye karar ga alƙalan kotun ƙoli.

Jim kaɗan bayan haka ne, kotun ta kori karar gaba ɗaya, wanda hakan ya ba Gwamna Fubara nasara a ɗaya daga cikin shari'o'in da yake fuskanta.

Kotu ta shirya yanke hukunci kan ƙarar APC

Bugu da ƙari, kotun koli ta tanadi hukuncinta kan karar da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) da ɗan takararta na gwamna, Patrick Tonye-Cole, suka ɗaukaka.

Kotun ta tanadi hukunci kan ƙarar Cole da jam'iyyar APC ne bayan kammala sauraron kowane ɓangare da ke cikin ƙarar, rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jigon NNPP ya fadi abu 1 da zai faru da alkalan Kotun Koli da Gwamna Abba ya yi rashin nasara

A baya dai kotun sauraron kararrakin zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara sun kori kararrakin da aka kalubalanci Fubara kana suka tabbatar da nasarar da ya samu a zaben Ribas.

Gwamma Abba ya yabawa Bola Tinubu

A wani rahoton kuma Abba Gida-Gida ya tabbatar da cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai tsoma baki a shari'ar zaben gwamnan jihar Kano ba.

Gwamnan ya ce duk da matsin lamba daga wasu tsiraru, Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ba su shiga lamarin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262