Da an Hana Abba Gida-Gida Mulkin Kano, Da Najeriya Ta Kama da Wuta, Inji Buba Galadima

Da an Hana Abba Gida-Gida Mulkin Kano, Da Najeriya Ta Kama da Wuta, Inji Buba Galadima

  • Jigon jam’iyyar NNPP ya bayyana kadan daga abin da ya hango da kotun daukaka kara ta hana NNPP mulkin jihar Kano
  • Ya da yanzu haka kasar nan ta kama da wuta idan aka haramtawa Abba Kabir Yusuf mulkin jihar da ke Arewa maso Yamma
  • An yanke hukuncin kan karar da aka shigar a kotun koli na sakamakon zaben Kano, an yi watsi da hukuncin kotunan baya

Najeriya - Fitaccen jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana ra’ayinsa da hangensa kan illar da ka iya biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a baya-bayan nan, musamman game da rikicin ‘yan takarar gwamna a jihar Kano.

A nasa ra'ayin, kasar na iya fuskantar tashin hankali idan har kotun koli ta yanke hukuncin tsige gwamna Abba Yusuf na jihar Kano a gagarumin hukuncin da ta yanke a ranar Juma'ar da ta gabata.

Kara karanta wannan

APC ta sadaukar da kujerar gwamnan Kano ga Abba Kabir ne don gudun fitina? gaskiya ta fito

Galadima ya mika sakon taya murna ga shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC bisa mutunta ‘yancin kan tsagin shari’a, musamman yadda lamarin ya shafi Nasir Gawuna, dan jam’iyyar APC.

Galadima ya fadi yadda aka ceto Najeriya
Da yanzu an dagula zaman lafiyar Najeriya, inji Galadima | Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Bayanin Buba Galadima

Da yake magana a Channels TV ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina taya mai girma shugaban kasa na rashin yin katsalandan a bangaren shari’a domin Najeriya za ta iya kamawa da wuta a yanzu idan abin da ya faru ranar Juma’a bai faru ba.
"Ina taya shi (Tinubu) murna saboda yana da karfin hali kuma za ka ga cewa zaman lafiya ya mamaye duk fadin Najeriya kuma darajarmu ta fito a idon duniya."

Legit Hausa ruwaito a baya cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne kotun koli ta yanke hukunci kan rigingimun gwamnoni takwas, inda ta soke hukuncin da kananan kotuna suka yanke a cikin kararraki uku.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

Yadda aka yi watsi da hukuncin baya

Daga cikin kararraki takwas, na Kano, Zamfara da Filato sun ba da mamaki yayin da kotun koli ta yi fatali da hukuncin da kotun kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka yanke na mayar da gwamnonin jihohin uku.

Kafin yanke hukuncin ranar Juma'a kan rikicin gwamnan Kano, tuni tashin hankali ya yi kamari a Kano, inda mabiya NNPP ke nuna damuwarsu.

Da yake magana a shirin Sunday Politcs na Channels TV, Galadima ya ce akwai wani shiri na kwace mulki daga hannun jam’iyyar NNPP a Kano kasancewar jam’iyyar ta kori APC daga kan karagar mulki a zaben da ya gabata.

Su Kwankwaso sun hada kai da Atiku, Obi

A wani labarin, jigon siyasar kasar nan ya labarta yadda 'yan siyasar Najeriya ke shirin kawo karshen mulkin Tinubu.

A cewarsa, su Peter Obi, Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar sun hada hadaka mai karfi a shirin zaben 2027.

'Yan Najeriya basu jima da yin zaben 2023 ba, ana ci gaba da shirin zaben da ke tafe nan da shekaru hudu masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.