2027: Atiku, Kwankwaso da Peter Obi Sun Hade Don Kafa Sabuwar Jam’iyya Don Kada Tinubu, In Ji Utomi
- Jigon siyasa a Najeriya ya bayyana yiwuwar kirkirar sabuwar jam’iyya a Najeriya da ‘yan siyasa za su yi a nan kusa kafin zabe
- Pat Utomi ya ce, akwai bukatar a hada kai tsakanin ‘yan siyasa domin samun shugabanni na gaba bayan mulkin APC na yanzu
- Ana ta jita-jita cewa, Kwankwaso, Obi da Atiku za su hada kai don samar da shugabanci na gari a zaben shekara ta 2027
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Najeriya - Masanin siyasa a Najeriya, Farfesa Pat Utomi a wata hira da gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun yanke shawarar kafa jam’iyyar hadaka don fitowa da karfi a gaba.
Da yake karin haske a tattaunawa, ya tattauna kan bukatar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Najeriya, inda ya jaddada cewa jam’iyyun da ake da su ba su yiwa jama’a hidima yadda ya kamata ba.
Ya kuma soki halin da siyasar Najeriya ke ciki, inda ya nuna rashin mayar da hankali wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Utomi ya kuma bayyana cewa gazawar jam’iyyar APC ba komai bane face saboda muguwar aniyar wasu mutane a cikin jam’iyyar.
Akwai bukatar kafa sabuwar jam’iyya
Ya kuma bayyana bukatar kafa sabuwar jam’iyya mai fayyatattun dabi’u da manufofi, tare da mai da hankali kan rikon amana da ci gaban kasa.
A cewarsa:
“Mu bar ta zabe a yanzu. Ya kamata mu ga yadda kasarmu za ta yi aiki ga kowa. Kuma mu samar da wata jam’iyyar siyasa da za ta iya fitar da al’amura a gaba domin dukkan al’ummar Najeriya su samu ra’ayi daya kan yadda za a magance matsaloli.
“Idan har muka samu wannan matsaya, za mu samu ‘yan Najeriyan da za su iya ba da kwazo a shugabanci, kuma ba za su kasance a kan abin da za su samu na kansu ba domin wannan hali cuta ce da ke durkusar da siyasar Najeriya.
"Abin da muke bukata shine mutanen da suka sadaukar da kansu don gina kasa mai girma tare da hangen ladansu har mutuwa".
Bugu da kari, ya bayyana tattaunawa da jiga-jigan siyasa daban-daban da shugabannin kungiyoyin siyasa ke yi game da kafa wannan sabuwar jam’iyya da kuma hada kai a zabe mai zuwa nan da 2027.
Jita-jita da ake yadawa kan siyasar gobe
A tun farko, jam’iyyar hamayya ta LP ta yi na’am da shawarar da Atiku Abubakar ya kawo na cewa akwai bukatar jam’iyyun adawa su hada-kai.
A ranar Alhamis, Punch ta kawo rahoto cewa LP ta yi maraba da kiran da ‘dan takaran PDP ya yi, jam’iyyar ta ce wannan abin a duba ne.
Amma jam’iyyar NNPP ta ce za ta goyi bayan hadin-kan ne da idan Atiku Abubakar zai bi bayan dan takaranta watau Rabiu Musa Kwanwaso.
Asali: Legit.ng