Tsohon Shugaban Soja Janar IBB Ya Fadi Muhimmin Tsarin Da Ya Fi Dacewa da Dimokuradiyyar Najeriya

Tsohon Shugaban Soja Janar IBB Ya Fadi Muhimmin Tsarin Da Ya Fi Dacewa da Dimokuradiyyar Najeriya

  • Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya yi magana kan tsarin jam'iyyun siyasa a ƙasar nan
  • Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa ƴan Najeriya ba za su taɓa amincewa da tsarin jam'iyya ba a ƙasar nan
  • IBB ya bayyana cewa tsarin jam'iyyyun biyu shi ne wanda yafi dacewa da ƙasar nan domin sauƙinsa da kuma kawar da ruɗani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ƴan Najeriya ba za su amince da tsarin jam’iyya ɗaya ba.

Sai dai ya ce tsarin jam’iyyu biyu shi ne mafi alheri ga Najeriya, cewar rahoton PM News.

IBB ya magana kan jam'iyyu a Najeriya
IBB ya ce tsarin jam'iyyu biyu ya fi dacewa da Najeriya Hoto: Facebook
Asali: UGC

Tsohon shugaban na mulkin sojan wanda ya mulki ƙasar nan daga shekarar 1985 zuwa 1993, ya faɗi haka ne a ranar Juma’a a lokacin wata hira da gidan talabijin na Channels tv a shirinsu na 'Inside Sources'.

Kara karanta wannan

"Shi ba dan jihar nan ba ne": Wike ya bayar da karin haske kan rikicinsa da Gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na kasance a mulkin soja, kuma ƴan Najeriya na san ba za su yarda a yi jam’iyya ɗaya ba. Na kasance soja, kuma na san mulkin kama-karya ba shi da kyau kuma ba zai iya zama mai kyau a cikin jama'a ba.
"Yan Najeriya da na sani ba za su amince da tsarin jam'iyya ɗaya ba kuma za su yi ta yaƙar hakan har sai sun kawo ƙarshensa."

"Tsarin jam'iyyu biyu ya dace da Najeriya", IBB

Akan tsarin jam’iyyu biyu kuwa, IBB ya bayyana cewa:

"Nan da nan bayan samun ƴancin kai, Najeriya ta yi ta kai-kawo ga tsarin jam’iyyu biyu. Mafi yawan jam'iyyu sun kafa ƙawance don samun madafun iko. Hakan ya faru a jamhuriya ta farko da ta biyu. Ya sake bayyana a jamhuriya ta uku da kuma jamhuriya ta yanzu.

Kara karanta wannan

Sojoji za su ƙara karbe ragamar mulkin Najeriya nan gaba? Tsohon shugaba soja ya feɗe gaskiya

"A lokacin, mun yi imanin ƴan Najeriya suna iya tsarin jam’iyyu biyu domin yana rage ‘wahala’ da yawa da ruɗani. Kuna iya zaɓar daga A ko B."

IBB Ya Yi Magana Kan Dawowar Mulkin Soja

A wani labarin kuma, kun ji cewa tohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya ce yana da yakinin cewa ba za a sake samun katsalandan daga sojoji ba wanda zai kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya.

Tsohon shugaban ya ce mulkin soji ya sa Najeriya ta sami naƙasu daga asalin tsarin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng