Kwankwaso Ya Cimma Yarjejeniya da Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano? Gaskiya Ta Bayyana

Kwankwaso Ya Cimma Yarjejeniya da Tinubu Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kano? Gaskiya Ta Bayyana

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan hukuncin zaɓen gwamnan Kano
  • Ƙwankwaso ya musanta cimma yarjejeniya da Shugaba Tinubu gabanin yanke hukuncin zaɓen gwamnan na Kano
  • Jigon na jam'iyyar NNPP ya kuma bayyana rawar da zai taka a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), ya yi magana kan jita-jitar cimma matsaya da Shugaba Bola Tinubu kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.

Kwankwaso ya ce bai cimma matsaya da Shugaba Bola Tinubu ba, ko kuma waninsa dangane da sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke kan rikicin zaɓen na gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli kan zaben Kano: Kwankwaso ya magantu, ya aika sako ga yan Najeriya

Kwankwaso ya musanta cimma yarjejeniya da Tinubu
Kwankwaso ya yi magana kan yarjejeniya da Tinubu Hoto: Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin cewa ya cimma yarjejeniya da Tinubu a gabanin yanke hukuncin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Kwankwaso ya ce kan yarjejeniya da Tinubu?

Da yake magana da BBC Hausa, Kwankwaso ya bayyana cewa:

"Abin da ya faru a kotun ƙoli darasi ne a gare mu baki ɗaya. Na san cewa ina alheri ga kowa. Tsawon lokaci, ban yi wa kowa komai ba. Kuma kowa zai girbi abin da ya shuka. A iyakar sanina ban cimma matsaya da kowa ba.
"Abin da na sani shi ne, Shugaba Bola Ahmed Tinubu mun yi zamani tare. Na shiga siyasa lokaci guda da shi a SDP. Sannan ya zama Sanata, ni kuma na zama mataimakin kakakin majalisar wakilai. A shekarar 1999 shi ne abokin aikina a matsayin gwamnan jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gawuna ya yi magana kan hukuncin kotun koli, ya tura muhimmin sako

"Mun kafa jam’iyyar APC tare kuma mun taka rawa sosai a fafutuka da suka biyo baya. Ya kamata mutane su sani cewa karya tana da gajeriyar rayuwa. Duk da makircin da mutanen suka yi, alƙalai sun yi abin da ya dace.
"Babu matsala. Suna da jam'iyyarsu, muna da tamu. Za mu yi aiki tare a inda ya cancanta. Dangane da batun shiga gwamnati lokaci ne kawai zai iya tantancewa.”

Kwankwaso ya kuma ce ba zai mallake gwamnan Kano ba, yana mai nuna da cewa zai ba shi shawara ne kawai a inda ya dace.

Gawuna Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙoli

A wani labarin kuma,.kun ji cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi martani kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan Kano.

Gawuna ya bayyana cewa ya amince da hukuncin domin haka Allah maɗaukakin Sarki ya so.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng