Gawuna Ya Yi Magana Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Tura Muhimmin Sako
- Ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi magana kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke
- Gawuna ya bayyana cewa ya amince da hukuncin wanda ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Ƙabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar
- Gawuna ya yi addu'ar Allah ya ta yi gwamnan riƙo tare da ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Kano, ya ce ya amince da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan shari'ar gwamnan jihar a matsayin hukuncin Allah.
Gawuna ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar BBC Hausa.
Gawuna da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP) sun yi ta shari'a bayan zaɓen gwamna a watan Maris na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Juma’a ne kotun ƙoli ta tabbatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano.
Me Gawuna ya ce kan hukuncin?
A hirar da BBC ta yi da shi, Gawuna ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke hukuncin Allah ne, yana mai cewa ya amince da shi da gaskiya.
A kalamansa:
“Wannan hukunci hukuncin Allah ne kuma mun yarda da shi. Kamar yadda muka yi addu'a cewa idan alkhairi ne Allah ya yi mana idan kuwa ba alkhairi ba ne ya musanya shi da mafi alheri. Muna da yaƙinin Allah ya amsa addu'o'inmu. Shi ne Mai hikima. Muna godiya ga Allah maɗaukakin sarki.
"Wannan shi ne abin da ya kamata duk shugabanni su yi bayan kammala shari'a a kotu. Tun kafin a fara shari'ar na yi masa fatan alheri. Addu'ar mu a kullum muna roƙon Allah ya sa shi zama shugaba mai adalci ga kowa, musamman a yanzu da aka tabbatar da shi a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar. Duk ɗan ƙasa mai kishi ya kamata yayi wannan addu'a."
Gwamna Abba Ya Yi Martani Kan Hukuncin Kotun Ƙoli
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi martani kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke.
Gwamnan ya miƙa.godiyarsa ga Allah bisa nasarar da ya samu a kotun ƙoli.
Asali: Legit.ng