An Tsame Ni Daga Zargi, Abba Kabir Ya Yi Godiya Bayan Hukuncin Kotun Koli, Ya Tura Sako
- Bayan yanke hukuncin Kotun Koli, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan takaddamar da ta zo karshe
- Gwamnan ya ce ya ji daɗin hukuncin inda ya yi godiya ga jama'ar jihar Kano da Najeriya baki daya
- Yusuf ya ce ya ji matukar dadi ganin yadda aka tsame sunansa daga zarge-zargen magudin zabe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi martani bayan yanke hukuncin Kotun Koli a Abuja.
Abba Kabir ya ce ya ji dadi bayan kotun ta tsame shi daga zargin badakala a zabe, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Mene Abba Kabir ya ce kan hukuncin?
Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Juma'a 12 ga watan Janairu bayan yanke hukuncin zaben a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf ya ce ya ji matukar dadi ganin yadda aka tsame sunansa daga zarge-zargen magudin zaben da aka gudanar a watan Maris.
Ya ce:
"Na ji matukar dadi, kamar yadda kuke gani mutane na murna da jin dadi, wanda hakan ya karamin farin ciki.
"Ina matukar jin dadi kan hukuncin Kotun Koli da aka gudanar a yau 12 ga watan Janairu.
"Wannan hukuncin kotun ya tabbatar min da cewa babu wata badakala da aka yi a zaben da aka gudanar."
Wane sako Abba Kabir ya aike?
Abba ya ce su na ta cewa akwai kuri'u wadanda ba su inganta ba don babu sitamfi a jikinsu, amma kotun ta yi hukunci a kan haka, Daily Post ta tattaro.
Ya kara da cewa:
"Na samu natsuwa saboda na fita daga zargi, an kawo karshen matsalar a yau.
"Ina godiya ga mutanen Kano da su ke min addu'a tun farkon watanni bakwai da na hau mulkin jihar.
"Ba iya mutanen Kano ba, ina godiya ga jama'ar Najeriya da ma duniya baki daya, nagode muku."
Murna ta barke a Kano bayan nasarar Abba Kabir
A wani labarin, Murna ta barke a Kano bayan nasarar Gwamna Abba Kabir a Kotun Koli a yau Juma'a 12 ga watan Janairu.
Kotun ta yi fatali da hukuncin Kotun Daukaka Kara da ta rusa zaben gwamnan a kwanakin baya.
Dan takarar jam'iyyar APC a jihar, Nasiru Gawuna shi ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Maris.
Asali: Legit.ng