Bidiyon Yadda Murna Ta Barke Bayan Nasarar Gwamna Abba Kabir a Kano, Bayanai Sun Fito
- Yayin da aka yanke hukuncin zaben jihar Kano, matasa da mata sun fito murna a titunan Kano
- Mata da matasa har ma da manyan mutane su na yi ihu tare da murna bayan nasarar Gwamna Abba Kabir
- Hakan na zuwa ne bayan nasarar da Kotun Koli ta bai wa Abba Kabir a yau Juma'a a birnin Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Yayin da aka yanke hukuncin Kotun Koli a Kano, jama'a sun fita cikin gari don murnar nasarar Abba Kabir.
A yau Juma'a ce 12 ga watan Janairu Kotun Koli ta raba gardama a shari'ar zaben gwamnan jihar.
Yadda ake murna a Kano bayan nasarar Gwamna Abba Kabir
An gano mata da matasa na murna a cikin wani faifan bidiyo da gidan talabijin Channels TV ta fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mene dalilin yin murnar a Kano?
A faifan bidiyon an gano mata da maza da matasa har ma da dattawa su na murnar samun nasarar a kan tituna.
An jiyo su na murna da cewa "Kano sai Abba", "Kano sai Abba" yayin da masu ababawan hawa ma ke nuna jin dadinsu.
Wannan na zuwa ne bayan sanar da Gwamna Abba Kabir a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kano.
Kotun yayin hukuncinta, Kotun ta mayar wa Gwamna Abba Kabir kuri'un da aka zaftare masa a Kotun Daukaka Kara a kwanakin baya.
Har ila yau, ta ce kasancewa dan jam'iyya ko sabanin haka wannan matsalar jami'yya ce tun kafin gudanar zabe.
Daga bisani, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan hukuncin Kotun Koli da ta ba shi nasara.
Abba ya bayyana jin dadinsa kan wannan nasara da ya samu tare da yi wa Allah godiya.
Kotun Koli ta yi hukunci a Kano
A wani labarin, Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano.
Kotun ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan daukaka kara da sauraran kararrakin zabe a baya.
Wannan hukunci ya tabbatar da korar karar dan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna a zaben da aka gudanar a watan Maris.
Asali: Legit.ng