Kano: Gwamna Abba Ya Maida Martani Bayan Kotun Koli Ta Yanke Hukunci, Ya Gode Wa Allah
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maida martani a karon farko bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaben gwamnan Kano
- Ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, kotun koli ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kana ta tabbatar masa da kujerar gwamna
- A kalamansa na farko, Gwamna Abba ya miƙa godiyarsa ga Allah yayin da masoya da mambobin NNPP suka ɓarke da murna
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya maida martanin farko jim kaɗan bayan kotun koli ta yanke hukunci kan taƙaddamar zaɓen gwamnan jihar.
A wani ɗan gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter, Gwamnan ya miƙa godiya ga Allah bisa nasarar da ya samu a kotun koli.
Yayin da take yanke hukunci, kotun kolin Najeriya ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, sannan ta tabbatar da Abba a matsayin halastaccen gwamnan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mintuna kaɗan bayan haka ne, Gwamna Abba ya garzaya shafinsa ya rubuta, "Alhamdulillah, Alhamdulillah" watau "Mun gode wa Allah, mun gode wa Allah."
Kotun koli ta raba gardama a shari'ar zaben Kano
Legit Hausa ta kawo muku rahoto a ɗazu cewa kotun koli ta tabbatar da nasarar Abba Kabir na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.
Kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ta rushe hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da kotun zaɓe, waɗanda suka kori Gwamna Abba daga kan madafun iko.
A hukuncin, mai shari'a Okoro, ya bayyana cewa kotun zaɓe ta yi kuskure da ta kwashe kuri'u 165,663 daga kuri'un Abba saboda kawai babu hatimi da sa hannun jami'an INEC.
Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Villa
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya gana da mambobin kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
Gwamnan jihar Imo kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodinma, ne ya jagorance su zuwa wurin ganawar yau Jumu'a.
Asali: Legit.ng