Ciki Ya Duri Ruwa Yayin da Ake Saura Awanni Kadan a Yanke Hukunci a Kano da Zamfara da Jihohi 6
- Ana ci gaba da zaman dar-dar a Kano yayin da yau ake dakon hukuncin karshe a shari’ar zaben jihar
- A yau Juma’a ce 12 ga watan Janairu Kotun Koli za ta raba gardama a jihohi takwas da ake shirin yanke hukunci
- Jihohin sun hada da Kano da Zamfara da Plateau da Legas da Bauchi da Cross River da Abia da kuma Ebonyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Yayin da ake zaman dar-dar a jihohin Kano da Zamfara da Plateau da sauransu, an tsaurara tsaro.
A yau Juma’a ce 12 ga watan Janairu Kotun Koli za ta raba gardama a jihohi takwas da ake shirin yanke hukuncin karshe.
Wasu jihohi ne za a yanke hukuncin?
Jihohin sun hada da Kano da Zamfara da Plateau da Legas da Bauchi da Cross River da Abia da kuma Ebonyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jihar Kano wacce ita ce shari’ar da tafi daukar hankulan ‘yan Najeriya gaba daya, Daily Trust ta tattaro cewa ana ta zaman dar-dar da cece-kuce kan shari’ar.
Yayin da ake cikin wannan hali, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya tsaf don dakin tashin-tashina a jihar.
Gumel ya ce sun baza jami’an tsaro a wurare na musamman a Kano inda ya gargadi masu son tada kayar baya, cewar Leadership.
Wane tanadi 'yan sanda su ka yi?
Da aka tambaye shi ko za a iya sanya dokar ta baci, sai ya ce ba dole ba ne amma dai za su dakile duk wasu masu son ta da hankali.
Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar, Hashimu Dogonruwa ya ce su na da tabbacin wannan nasara ta su ce da yardar Allah.
A bangarenshi, sakataren yada labaran APC a jihar, Ahmad Aruwa ya ce da yardar Allah nasara ta APC ce ganin yadda suka mika shaidu masu karfi.
A Plateau da Zamfara kuwa, jami'an ‘yan sanda a jihohin sun tabbatar da wadatar jami’an tsaro don kawo zaman lafiya a jihohin.
Haka a jihohin Legas da Bauchi, dukkan shirye-shirye sun kankama don tabbatar da zaman lafiya bayan yanke hukuncin.
PDP ta koma ga Allah a Plateau
Kun ji cewa, jam'iyyar PDP a jihar Plateau ta mika lamuranta ga ubangiji yayin da ake shirin yanke hukunci.
Jam'iyyar ta bukaci magiya bayanta su tashi da azumi da kuma addu'o'i don neman nasara.
Asali: Legit.ng