Gwamna Zulum Ya Yi Babban Rashi, Mai Magana Da Yawunsa, Gusau, Ya Rasu
- Mai taimakawa na musamman bangaren watsa labarai da tsare-tsare na Gwamna Babagana Zulum, Mallam Isa Gusau, ya rasu sakamakon rashin lafiya
- Yayin da kawo yanzu gwamnatin Borno ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, wani rahoto ya yi ikirarin cewa ya rasu a Indiya ne, wani kuma ya ce a Landan ya rasu yayin masa magani
- Gusau shine mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima lokacin da ya ke gwamnan jihar ta Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Maiduguri, Borno - Rahotanni da suka fito na cewa mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Mallam Isa Gusau, ya rasu a wani asibiti da ke kasar Indiya.
A cewar This Day, Gusau shine mai magana da yawun Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasan Najeriya, a lokacin da ya ke gwamna a jihar Borno. An rahoto cewa kakakin gwamnan ya shafe kimanin wata guda a wani asibiti a Indiya yana jinyar wani ciyo da ba a bayyana ba kawo yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ina mai magana da yawun Gwamna Zulum ya rasu
Jaridar ta rahoto cewa Gusau ya yi numfashinsa na karshe a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, a wani asibitin kwararru a New Delhi, babban birnin Indiya, a cewar wata majiya da nemi a boye sunanta.
A cewar majiyar:
"Mun rasa Isa, ya suma na kimanin kwana uku, dukkanmu muna masa addu'ar samun sauki, amma abin bakin ciki ya rasu da yamma yau (jiya) a asibiti a New Delhi, Indiya."
Ta yaya hadimin Zulum ya rasu?
This Day a cikin rahotonta ta kara da cewa marigayi Gusau bai dena yin ayyukansa ba har ma a gadon asibiti a Indiya, ta kara da cewa ya fitar da sanarwar manema labarai da dama.
Sai dai, Leadership, ta ambaci wata majiya a rahotonta da ke cewa hadimin gwamnan ya rasu a wani asibiti da ke Landan, inda ake masa magani kan wani rashin lafiya da ya dade yana fama da ita.
Kawo yanzu gwamnatin jihar Borno ba ta riga ta fitar da sanarwa ba a hukumance dangane da rasuwar hadimin gwamnan, kuma ba a riga an gano ko an dawo da gawansa Najeriya ba don masa jana'iza.
Asali: Legit.ng