Bayanai Sun Fito Kan Haduwar Abba Da Ministar Tinubu Kafin Hukuncin Kotun Koli

Bayanai Sun Fito Kan Haduwar Abba Da Ministar Tinubu Kafin Hukuncin Kotun Koli

  • Doris Anite ta kai ziyara zuwa jihar Kano domin yin wasu aiki inda ta hada da manyan jami’an gwamnati
  • Abba Kabir Yusuf ya bayyana makasudin zama da ministar kasuwancin a gidan gwamnatin jihar Kano
  • Dr. Anite ta hadu da irinsu Mai girma Aminu Abdussalama Gwarzo da Sakataren gwamnati na rikon kwarya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Abba Kabir Yusuf ya hadu da ministar kasuwanci a Najeriya, Dr. Doris Anite a karshen makon nan.

Mai girma gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da haduwar a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano ana gobe hukuncin kotun koli Hoto: Abba Kabir Yusuf, supremecourt.gov.ng
Asali: Facebook

Ministar kasuwanci a jihar Kano

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, Doris Anite ta zo Kano a ranar 11 ga watan Junairu, 2024 ne domin wani aiki.

Tattaunawar gwamna Abba Kabir Yusuf da ministar kasuwancin kasar ta shafi yadda za a bunkasa kasuwanci.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Gwamonin APC sun dauki mataki ana tsaka da binciken badakala, bayanai sun fito

Dr. Doris Anite ta nuna akwai damammkin harkar kasuwanci da-dama a jihar Kano wanda za su iya kawo cigaba.

Kano na jiran hukuncin kotun koli

Ziyarar ta zo ne daidai lokacin da ake sauraron hukuncin da kotun koli za ta yanke a game da zaben gwamnan Kano.

Gwamna Abba da aka fi sani da Abba Gida Gida ya daukaka kara bayan kotun daukaka kara ta tunbuke shi.

Abba ya halarci taron shari'an Kano

Kafin nan kuma mai girma gwamnan ya halarci taron masana shari’a na shekarar 2024.

Gwamna da mataimakinsa da sakataren gwamnati na rikon kwarya da AGF sun halarci taron da aka yi a jihar Kano.

Kamar yadda yake fada a shafin X, Abba ya yi amfani da damar wajen kira ga masana shari’a su dage wajen yin adalci.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsu za ta cigaba da kokarin ganin ‘yancin bangaren shari’a a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Nesa ta zo kusa: Kotun koli ta sanya ranar yanke hukuncin kan zaben gwamnan Kano, Bauchi da wasu jihohi 5

Za a tsige gwamnan Kano a kotun koli?

Zuwa yanzu masoya sun dage wajen yi wa gwamnan da NNPP addu'ar samun nasara a shari'arsa da ke kotun koli.

Magoya bayan APC da sauran 'yan adawa kuwa sun ce ya bar karagar mulki kenan daga gobe saboda kotu za ta tunbuke shi.

PDP, LP da NNPP za su hada-kai?

Kun ji labari abubuwa za su iya canzawa daga yau musamman idan APC ta karbe mulkin Kano da wasu jihohi a kotun koli.

Jagororin jam’iyyun hamayya sun fara daukar shawarar Atiku Abubakar na yakar Bola Tinubu a zabe mai zuwa na 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng