Jam'iyyar APC Ta Aike da Sako Mai Muhimmanci Yayin da Kotun Koli Ke Dab da Yanke Hukunci
- Jam'iyyar APC a jiha Plateau ta aike da muhimmin saƙo yayin da ake jiran hukuncin da kotun ƙoli za ta yanke
- Kotun ƙolin dai ta sanya ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukunci kan shari'ar Gwamma Mutfwang da Nentawe Yilwatda
- Jam'iyyar ta buƙaci magoya bayanta da su kwantar da hankulansu inda ta ce a shirye take ta amince da hukuncin da kotun ƙolin za ta yanke
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Jam’iyyar APC reshen jihar Plateau ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu yayin da kotun ƙoli za ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar.
Kotun ƙolin ta sanya ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan ƙarar da Gwamna Caleb Mutfwang ya shigar na ƙalubalantar tsige shi da kotun ɗaukaka ƙara ta yi.
Jam’iyyar APC ta Plateau, a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta, Mista Sylvanus Namang, ya fitar, ta buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su guji duk wani abu da ya saɓa wa al’adar jam’iyyar, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane kira jam'iyyar APC ta yi?
Namang ya ce jam’iyyar APC ta yi amanna da kwanciyar hankali da zaman lafiya a dukkan harkokinta, duk kuwa da irin halin da ake ciki, rahoton Leadership ya tabbatar.
A kalamansa:
"Ko wane hukunci kotun ƙoli ta yanke, jam’iyyar APC wacce ta kasance mai bin doka da oda da kuma kishin tsarin shari’ar mu, za ta yi maraba da sakamakon da aka samu cikin aminci.
"Jam’iyyar na son sake bayyana matsayinta kan mutunta kundin tsarin mulki da bin doka da oda, waɗanda su ne ginshiƙin dimokuraɗiyya da shugabanci na gari."
Jam’iyyar ta kuma buƙaci jami’an tsaro a jihar da su sa ido sosai don ganin an kiyaye doka da oda.
Kotun Koli Ta Sanya Ranar Raba Gardama a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ƙoli ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Plateau.
Kotun ƙolin ta sanya ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu domin raba gardama tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang na PDP da Nentawe Yilwatda na APC.
Asali: Legit.ng