Betta Edu: Shekarau Ya Yaba, Ya Fadi Abin da Ya Ragewa Tinubu Ya Aikata a Ofis

Betta Edu: Shekarau Ya Yaba, Ya Fadi Abin da Ya Ragewa Tinubu Ya Aikata a Ofis

  • Ibrahim Shekarau bai bari adawarsa ga gwamnatin APC ta hana ya yi wa Bola Ahmed Tinubu adalci ba
  • Tsohon gwamnan ya ji dadin dakatar da Betta Edu da rage ayarin shugaban kasa, iyalinsa da mataimakinsa
  • Shekarau ya nuna wannan mataki da Bola Ahmed Tinubu ya dauka zai sa masu mulki su dawo hayyacinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ibrahim Shekarau, ya jinjinawa matakin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na dakatar da Betta Edu daga bakin aiki.

A wata hira da aka yi da Ibrahim Shekarau a gidan talabijin Channels, Ibrahim Shekarau ya ce shugaban kasar ya yi abin a yaba.

Shekarau da Tinubu
Ibrahim Shekarau ya yabi Bola Tinubu Hoto: @MallamShekarau, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Malam Shekarau wanda ya yi gwamna a jihar Kano ya ce hukunta Dr. Betta Edu domin ayi bincike zai zama darasi ga masu mulki.

Kara karanta wannan

Duk da adawarsa, mataki 1 da Shugaba Tinubu ya dauka ya jawo Atiku ya yaba masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai rage kashe kudin gwamnati

A ranar Talata tsohon Sanatan Kano ta tsakiya ya tofa albarkaci a kan abubuwan da ke faruwa da Edu da kokarin rage facaka da kudi.

Game da sabon umarnin da Mai girma shugaban kasa ya bada na rage ayarin masu mulki, Malam Shekarau ya ce hakan ya yi daidai.

Shekarau wanda ya taba zama Minista yana ganin hakan zai sa kowa ya shiga taitayinsa.

"Abin da zan fara fada shi ne yabawa gwamnatin Tinubu a kan matakin farko da ta dauka.
Abin a yaba ne kuma ina tunanin zai zama darasi ga saura."

- Ibrahim Shekarau

Bayan rage kashe kudi wajen zirga-zirga a gwamnati, tsohon Ministan ilmin ya ce ya kamata a rage adadin Ministocin kasar.

Shekarau yana so a rage mukarraban Tinubu

‘Dan siyasar bai ganin ana bukatar rage wasu mutanen da Bola Tinubu ya ba mukami.

Kara karanta wannan

Ba kamar Buhari ba, Tinubu ya dauki mataki kan yawan kashe kudade a tafiye-tafiye, ya fadi dalili

"Wani abin da na ke sa rai shugaban kasan ya duba shi ne adadin masu rike da mukamai.
Ba a bukatar wasu daga cikin wadanda aka ba mukaman nan ba su. Gwamnati ta fito da mafi karanci ko yawan adadi (na masu mukami)."

- Ibrahim Shekarau

Atiku ya yabawa gwamnatin Tinubu

An samu rahoto cewa Atiku Abubakar ya yabi gwamnatin APC da aka yi waje da Dr. Betta Edu domin EFCC tayi cikakken bincike a kan ta.

‘Dan adawar ya ce bai dace tun farko tsohuwar kwamishinar ta zama Minista a gwamnati ba domin ba ta da cikakken kwarewa a aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng