Yanzun nan: Babbar Kotu Ta Raba Gardama, Ta Bayyana Halastaccen Sakataren PDP Na Ƙasa
- Babbar kotun birnin Abuja ta yanke hukunci kan taƙaddamar kujerar sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa
- Yayin yanke hukunci ranar Talata, kotun ta tabbatar da Sanata Samuel Anayanwu a matsayin sakataren PDP
- Mai shari'a Inyang Ekwo ya kuma hana INEC karɓan wani daban a matsayin sakataren babban jam'iyyar adawa in banda Anyanwu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta bayyana Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sahihin sakataren Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa.
Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya yanke wannan hukunci ranar Talata, 9 ga watan Janairu, 2024, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ya kuma bada umarnin hana jam'iyyar PDP naɗa wani sakataren riƙo yayin da wa'adin shekaru huɗu na Sanata Anyanwu bai kare ba sai shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar alkalin kotun, Sanatan ba zai bar kujerar sakataren PDP na ƙasa ba har sai ranar 25 ga watan Disamba, 2025 kamar yadda kundin tsarin jam'iyyar ya tanada.
Mai shari'a Ekwo ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na hana Anyanwu yin aikin ofishinsa ya saɓawa sashi na 47 (1) na kundin dokokin PDP na 2017 wanda aka yi wa garambawul, Channels tv ta ruwaito.
Kotun ta aike da saƙo ga INEC
Bugu da ƙari, Alkalin ya hana hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta amince da kowaye aka kai mata a matsayin sakataren PDP na ƙasa in banda Anyanwu.
Kamfanin dillancin labarai (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar 23 ga watan Nuwamba, 2023, kotun ta dakatar da PDP daga cire Anyanwu a matsayin sakataren har zuwa lokacin da zata yanke hukunci.
Takarar da Sanata Anyanwu ya tsaya a zaben gwamnan jihar Imo ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 ne ya hadddasa ruɗani kan kujerarsa ta sakataren PDP.
INEC ta kammala shirin zabe a Kano
A wani rahoton na daban INEC ta bayyana cewa ta kammala dukkan wasu shirye-shiryen gudanar da zaben cike gurbi na yan majalisar dokokin jihar Kano guda 3.
Kwamishinan zaben jihar, Abdu Zango, ya ce jami'ai sun shirya tsaf domin gudanar da sahihin zaɓe a watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng