Ba Kamar Buhari Ba, Tinubu Ya Dauki Mataki Kan Yawan Kashe Kudade a Tafiye-tafiye, Ya Fadi Dalili
- Yayin da ake kukan rashin kudi a Najeriya, Shugaba Tinubu ya dauki muhimmin mataki don rage yawan kashe-kashen kudade
- Tinubu ya dauki matakin rage yawan kashe kudaden da kaso 60 wanda ya shafi dukkan tafiye-tafiyen masu mukamai
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Talata 9 ga watan Janairu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya rage yawan kudade da ake kashewa a tafiye-tafiye cikin gwamnatinsa da kaso 60.
Tinubu ya bayyana haka ne a yau Talata 9 ga watan Janairu ta bakin kakakinsa, Ajuri Ngelale a Abuja.
Wace sanarwa Tinubu ya fitar?
Ngelale ya ce wannan na daga cikin hikimar Tinubu don rage yawan kashe kudade da ake yi a gwamnati, cewar NTA News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, Ngelale ya ce matakin zai shafi ofishin shugaban kasa da mataimakinsa da kuma matar shugaban kasa.
Sauran ofisoshin sun hada da na ministoci da kuma shugabannin hukumomin kasar da sauransu.
Sanarwar ta ce shugaban ya kuma rage yawan mutane da za su rinka tafiya da shi da kuma mataimakinsa.
Wasu ofisoshi dokar Tinubu ta shafa?
Har ila yau, an kayyade yawan wadanda za su kasance da matar shugaban kasa yayin tafiye-tafiye a gida da waje.
Sanarwar ta ce:
"Tinubu ya bukaci dukkan tafiye-tafiyen a rage su, wannan umarni ne ba shawara ba, mataimakin shugaban kasa da ma'aikatansa duk ya shafe su.
"Wannan umarni ya zai datse yawan kashe kudaden da kaso 60."
Tafiye-tafiyen kasashen waje:
- Shugaban kasa - mutane 20
- Mataimakinsa - mutane biyar
- Matar shugaban kasa - mutane biyar.
Tafiye-tafiyen cikin gida:
- Shugaban kasa - mutane 25
- Mataimakinsa - mutane 15
- Matar shugaban kasa - mutane 10, cewar Channels TV.
An hana Edu shiga fadar Tinubu don ganawa
A wani labarin, Fadar shugaban kasar Najeriya ta hana dakatacciyar Ministar jin kai da walwala, Betta Edu ganawa da Tinubu.
Bayan hana Ministar an kuma kwace takardar shaidar samun damar shiga fadar Aso Rock a jiya Litinin.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin Betta Edu da wawure wasu makudan kudade da aka ware don tallafawa marasa karfi.
Asali: Legit.ng